Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Bauchi Ta Sanya Dokar Hana Fita Na Awa 24 A Katagum
Daga Khalid Idris Doya
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya kakaba dokar hana zirga-zirga na tsawon awa 24 a karamar hukumar Katagum da ke jihar sakamakon tabarbarewar lamarin tsaro a garin Azare da kewayenta.
Idan za a tuna dai mun bada labarin da ke cewa masu zanga-zangar neman dawo da tallafin mai da kawo karshen matsin rayuwa rayuwa a ranar Litinin sun kutsa kai cikin sakatariyar karamar hukumar da ke Azare da gidan Gwamnatin jihar Bauchi (masaukin baki) da ke Azare tare da gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Baba Tela inda suka yi satar wasu kayayayyaki da kone-kone a wasu yankunan gami da lalata kadarori.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Muhammad Kashim ya fitar a ranar Litinin, na cewa, gwamnatin ta dauki wannan matakin ne sakamakon matsalolin tsaro da aka samu a Azare da kewayenta da ya janyo lalata kadarori jama’a da cin zarafi.
Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da sun zakulo wadanda suka saci kayan al’umma domin su fuskanci hukunci.
Ya ce, “Mai girma gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon awanni 24 a karamar hukumar Katagum kuma dokar za ta fara aiki nan take domin dakile lamarin.”
Gwamnan ya yi kira ga al’umma jihar da su ci gaba da kasancewa masu biyayya da doka da oda tare da kara bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai a irin wannan mawuyacin halin da kasa take ciki.