Hausa

SARAUTA: ANYI ZABEN DAGACIN JARKASA A MISAU.

Sarauta abace mai matukar muhimmanci ga tarin hikima dake ciki. Shi yasa ma alumma game da shuwagaba nin yankin kasar Jarkasa a karkashin masarautar Jarkasa ta karamar hukumar Misau dake jihar Bauchi, suka yi zaben dagacin da zai mulki jamaar Jarkasa.

Shugaban da ya jagoranci wannan zabe Hakimin Kasar Jalam Alh Sale Mohammed Jalam tare da mataimakinsa Hakimin Kasar Hardawa Alh Abubakar Garba Lili Da Wakilin Shugaban Karamar Hukumar Misau Hon Salisu Hussaini Dando Zannan Hardawa Mataimakin Chiyaman Harma Da Jamiyan tsaro na Kasar Misau su suka zama shaida a gurin zaben.

Alh Aminu Yusuf Jarkasa shi ya samu nasara da Kuria 29 cikin 32 na Kasar Jarkasa
Inda mabiyinsa Alh Hudu Yusuf ya samu Kuria 3.

Sabon Dagacin Kasar Jarkasa Alh Aminu Yusuf Mai Shekaru 50 .

Cikin Jawabinsa Shugaban Karamar Hukumar Misau Rt Hon Abubakar Ahmad Garkuwan Misau yataya Alh Aminu Yusuf murna ya kuma ja hankalinsa da ya rike yan’uwansa ya kuma rike amanan da Allah ya dora masa amar yadda Mahaifinsu ya zama a baya
daga karshe ya masa Addua na fatan Allah ya bashi ikon sauke nauyin da Allah ya dora masa.

5 thoughts on “SARAUTA: ANYI ZABEN DAGACIN JARKASA A MISAU.

Leave a Reply