Uncategorized

Dan Majalisa Mai Wakiltar Mazabar Azare/Madangala A Sikeli

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Azare/Madangala a majalisar dokokin jihar Bauchi Hon Zakariyya Sale Maigero, Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a majalisar dokokin jihar Bauchi ya cika wata shida a Majalisa a matsayin dan majalisa mai wakiltan Azare/Madangala.

A bisa wannan muke son jin ra’ayoyinku dangane da kamun ludayin wakilcinsa. Shin kwalliya ta fara biyan kudin sabulu ko yaya?

Ko za ku iya fadan wani abu da ya yi a cikin wadannan kwanakin?

Kuma a matsayinka/ke na dan kasa ka/kin gamsu da kamun ludayinsa ko akasin hakan?

Muna son Jin ra,ayi ba tare da cin mutumci ba, illa bayyana albarkacin baki zallah.

Saboda kundin tsarin mulki sashe na 39 ya ba ka dama ka fadi ra’ayinka a matsayin na dan kasa.

Muna tsumayar ra’ayoyinku da sharhinku.

Leave a Reply