Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Bakwai: Dagewa da Ibada a kwanaki goman karshe na Ramadhan

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

‘Yan’uwa kwanaki goman karshe na Ramadhan sun shiga, a cikinsu akwai alherai masu yawa, da falaloli masu yawa wadanda Allah ya kebance su da kwanakin.

Daga cikin kebantattun falaloli na wadannan kwanaki Annabi (saw) ya kasance yana kokari da damaran yin ibada fiye da yadda yake yi a sauran kwanakin watan, ya tabbata daga A’isha (ra) ta ce: ((Manzon Allah (saw) yana dagewa da Ibada a kwanaki goman karshe dagewan da ba ya yin irinsa a waninsu)) Muslim (1175).
Kuma ya tabbata ta ce: ((Idan goman karshe sun shiga Annabi (saw) ya kasance yana daura damara, yana raya darensa, yana tayar da iyalansa daga bacci)) Bukhari (2024) Muslim (1174).
A cikin wadannan Hadisai akwai bayanin falalolin wadannan kwanaki goma na karshen Ramadhan, saboda Annabi (saw) ya fi dagewa da Ibada a cikinsu fiye da sauran kwanakin watan, wannan kuwa ya kunshi dagewa a kan aikata dukkan nau’o’in ibada; na Sallah, karatun Alkur’a, zikiri, sadaka da sauransu, saboda Annabi (saw) ya kasance yana nisantar iyalinsa, don ya samu cikakken lokaci na ibada da zikiri, kuma ya kasance yana raya darensa gaba dayansa da Sallah, da karatun Alkur’ani da ambaton Allah da zuciya da harshe da gabobi, saboda darajar wadannan kwanaki, da kuma neman daren Lailatu Qadr, wacce duk wanda ya yi Sallan dare a cikinta, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa, kamar yadda ya tabbata daga Abu Huraira (ra), Annabi (saw) y ace: ((Duk wanda yay i Sallar dare a daren Lailatul Qadr, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)). Bukhari (1901), Muslim (760).

Daga cikin abin da yake nuna falalar wadannan kwanaki Annabi (saw) ya kasance yana tayar da iyalansa daga bacci, don su tashi su yi Sallah da zikiri, don su ribaci wadannan darare masu albarka, saboda dama ce a rayuwa, ganima ce daga Allah, bai kamata Mumini mai hankali ya yi sakaci har wannar dama ta kubuce masa shi da iyalansa ba, saboda darare ne kirgaggu, ta yiwu a cikinsu bawa ya yi gamon katar, wanda zai zamo sanadin samun rabo gare shi a Duniya da Lahira.

Lallai yana daga cikin hasara mai girma ka ga mutane masu yawa suna bata lokaci a cikin wadannan kwanaki, a kan abin da ba shi da amfani, su kwana suna bata dare a wasanni da kallace – kallace, amma idan lokacin Sallar dare ta yi sai su yi bacci, ko kuma su cigaba da wasanninsu, sai su rasa alherin da a shekara sau daya kawai ake samunsa. Duk wannan yana daga cikin wasan da Shaidan yake yi da bayi, yake toshe musu hanyar alherai.

Mai hankali ba zai yi wasa har Shaidan ya hana masa samun alherai da falaloli da suke cikin wadannan kwanaki ba.

Daga cikin falalolin wadannan kwanaki akwai yin I’itikafi, saboda Annabi (saw) ya kasance yana yin I’itikafi a cikinsu.
I’itikafi shi ne lazimtar Masallaci don shagaltuwa da Ibada kadai. I’itikafi yana daga cikin Sunnoni da suka zo a cikin Alkur’ani da Sunnar Annabi (saw), Allah ya ce: {Kada ku sadu da su (matanku) alhali kuna I’itikafi a Masallatai} [al-Baqarah: 187].
Annabi (saw) ya yi I’itikafi, Sahabbansa sun yi a bayansa, ya tabbata daga A’isha (ra) ta ce: ((Lallai Annabi (saw) ya kasance yana yin I’itikafi a goman karshe na Ramadhan, har ya rasu. Sa’annan matansa sun yi I’itikafi a bayansa)) Bukhari (2026), Muslim (1172).

Manufar I’itikafi ita ce mutum ya yanke daga komai don ya shagaltu da Ibada kadai a Masallaci, don neman falalar Allah da ladansa, da kuma neman dacewa da daren Lailatul Qadr. Saboda haka ake so mai I’itikafi ya shagala da zikiri, da karatun Alkur’ani, da nafilfili na Sallah, kuma ya kamata ya nisanci duk abin da ibada ba, da abin da bai shafe shi ba, na surutu a kan lamarin Duniya. Babu laifi idan ya yi magana a kan abubuwan da akwai Maslaha a cikinsu, ko akwai bukata. Ya tabbata daga Safiyya (ra) ta ce: ((Annabi (saw) ya kasance yana yana I’itikafi sai na zo na ziyarce shi da daddare, na yi magana da shi, sai na koma gidana, sai Annabi (saw) ya tashi tare da ni don ya mayar da ni)) Bukhari (3281), Muslim (2175).

Haramun ne mai I’itikafi ya sadu da iyali, da yin abin da suke gabanninsa; sunbanta, shafa da sha’awa da sauransu, saboda fadin Allah: {Kada ku sadu da su (matanku) alhali kuna I’itikafi a Masallatai} [al-Baqarah: 187].

Amma fitan mai I’itikafi daga Masallaci ya kasu kashi uku:
Na farko: Fitan da ya zama dole:
Kamar fita zuwa bayan gida, don biyan bukata, wankan janaba, Alola, ko fita don cin abinci. Idan ya zama babu bayan gida a Masallacin, kuma babu wanda zai kawo masa abinci da zai ci, to babu laifi ya fita, saboda ya zama dole.
Amma idan zai yiwu a kawo masa abinci ya ci a Masallacin, kuma a Masallacin akwai bayan gida da zai shiga ya biya bukatansa, to babu bukatar ya fita.

Na biyu: Fita saboda aikin da’a:
Kamar fita saboda gai da maras lafiya, ko halartar Sallar jana’iza da makamancinsu, to wannan ba zai fita ba, sai dai idan ya shardanta hakan tun lokacin fara I’itikafin, don haka babu laifi.

Na uku: Fita ga abin da ya saba ma I’itikafin:
Kamar fita don yin kasuwanci, ko don saduwa da iyali; Jima’i da abin da ke da alaka da shi, to wannan bai halasta ba, ko da kuwa ya shardanta hakan, saboda yana kore manufar I’itikafin.

Daga cikin kebantattun falaloli na wadannan kwanaki, a cikinsu daren Lailatul Qadr take, daren da ya fi wata dubu.

Don haka ya ku ‘yan’uwa, ku kiyaye darajan wadannan kwanaki, ku dage da ibada a cikinsu, ku nemi daren Lailatul Qadr. Lallai wadannan kwanaki suna da tsada, kar ka sake ka yi asaransu.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita aiyukan da’a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ka sa mu dace da daren Lailatul Qadr.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al’umma da tausayin talakawa.

2 thoughts on “DARUSAN RAMADHAN

Leave a Reply