DARUSAN RAMADHAN
Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia
Darasi na Goma: Hikimar Shar’anta Azumi
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Alal hakika Ibada da Allah ya umurce mu da yinta, kuma ya halicce mu don ita tana da hikimomi masu yawan gaske, da fa’idoji masu amfani na zahiri da na ma’ana, saboda Allah Madaukaki mai ilmi ne, kuma mai hikima ne, don haka ya zama akwai hikima cikin halittarsa da Shari’arsa; na umurni da hani, da ibadu da ya wajabta ma bayi.
Shar’anta Azumi, da farlanta Azumin Ramadhan yana da hikimomin masu yawa, wadanda suka sa Azumin ya zama cikin Rukunan Muslunci.
Azumi ibada ce da take kusatar da bawa ga Ubangijinsa, ta hanyar hana ransa abubuwan da take so na abinci da abin sha da biyan sha’awarsa ta saduwa, saboda abin da Ubangijinsa yake so, a cikin haka gaskiyar imaninsa yake bayyana, da cikar bautarsa ga Ubangijinsa, da karfin soyayyarsa gare shi. Saboda mutum ba ya barin abin da yake so sai saboda abin so wanda ya fi wancan girma. Shi Mumini a lokacin da ya san ana samun yardar Allah a Azumi, sai ya fifita samun yardar Allah a kan abin da ransa yake so, sai ya bar abin da ransa yake so don ya aikata abin da Allah yake so.
Daga cikin hikimomin farlanta Azumin, shi sababi ne na samun Taqwa da tsoron Allah, Allah ya ce:
{Ya ku wadanda suka yi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, don ku samu tsoron Allah} [al-Baqara: 183].
Saboda haka ne mai Azumi aka umurce shi da aikata aiyukan da’a, da nesantar sabo da aiyukan zunubi, Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda bai bar fadin karya da aiki da ita ba, da aikin jahilci to Allah ba ya bukatar ya bar cin abincinsa da abin shansa)). Bukhari (6057).
Shi Mumini mai Azumi, da zaran ya yi tunanin aikata sabo sai ya tuna cewa; yana Azumi, sai ya bari, shi ya sa Annabi (saw) ya umurci mai Azumi, idan wani ya zage shi, ko ya neme shi da fada, to ya ce: ni mai Azumi ne.
Daga cikin hikimar farlanta Azumi, tunanin mutum da zuciyarsa za su shagala da amboton Allah da tuna Allah, saboda ta rabu da abubuwan sha’awa da suke dauke hankali, na ci da sha da saduwa, wadanda suke makantar da zuciya, shi ya sa Annabi (saw) ya koyar da sassauta cin abinci, inda ya ce: ((Dan’adam bai cika mazubi mafi sharri kamar cikinsa ba. ‘Yan lomomi sun ishi dan’adam wadanda za su tsayar masa da bayansa, idan ya zama dole to ya kasa cikin kashi uku, daya na abincinsa, daya na abin shansa, daya na numfashinsa)). Tirmiziy (2380), Ibnu Majah (3349).
Daga cikin hikimar farlanta Azumi, mawadaci zai san girman ni’imar Allah a kansa, ta yadda ya wadata shi da abinci da abin sha da aure, alhali da yawa sun rasa wannar ni’ima. Don haka sai ya gode ma Allah a kan wannar ni’ima, kuma zai tuna ‘yan’uwansa talakawa wadanda suke kwana cikin yunwa, sai ya taimaka musu da sadaka da kyauta, ya ba su abinci da abin sha da tufafi. Wannan ya sa Annabi (saw) ya fi kyauta a Ramadhan fiye da kowane lokaci, ya fi yin kyautan a lokacin da Jibril (as) yake haduwa da shi suna darasin Alkur’ani, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Ibnu Abbas, duba Bukhari (4997), Muslim (2308).
Daga cikin hikimar farlanta Azumi, hanyoyin jini a jikin mutum suna kuntacewa saboda yunwa da kishirwa, sai hanyoyin gudanar Shaidan a jikin mutum su kuntace, saboda yana gudana ne a magudanan jini, kamar yadda ya tabbata daga Annabi (saw) ya ce: ((Lallai Shaidan yana gudana a jikin mutum ta magudanan jini)) Bukhari (2039), Muslim (2174). sai Azumi ya toshe hanyoyin wasiwasin Shaidan, ya tare wa mutum hanyoyin motsa sha’awa da tunzuran fushi. Shi ya sa Annabi (saw) ya ce: ((Ya ku matasa, wanda ya samu ikon aure to ya yi, saboda yana rintse ido, kuma yana kare farji. Idan kuma bai samu iko ba to ya lazimci Azumi, don makari ne gare shi)). Bukhari (5065) da Muslim (1400).
Azumi yana da fa’idoji masu yawa, ta bangaren kiwon lafiya, da kuma bangaren samun karfin rai, da karfin zuciya da samun tarbiyya ta juriya, da iya hadiye fushi, da kuma tarbiyya a kan nisantar girman kai da saukin hali, don yawan cin abinci da koshi da yawan saduwa, yana haifar da munanan dabi’u na alfahari da jiji da kai da girman kai wa mutane.
Don haka zuciya da rai suna bukatar ibadu da za su tsarkake su, su sa su zama bayin Allah masu taushi da kankan da kai ma Allah Madaukaki, Azumi kuma yana daga cikin manyan Ibadu masu samar da wannar tarbiyya, da tsarkake zukata da gyaran halaye.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu.