Uncategorized

Gwamna Bala, Inuwa, Wase, Yuguda Sun Halarci Daurin Auren Diyar Sarkin Bauchi


Daga Khalid Idris Doya 


Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu, a ranar Juma’a, ya karbi bakwancin gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, gwamna Muhamadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin tarayya, Hon. Idris Wase wadanda suka kasance a jihar Bauchi domin shaida daurin auren ‘yarsa, Fatima Rilwanu Sulaiman Adamu.


Babban Limamin Bauchi, Imam Bala Ahmad Babban Innah shi ne ya jagoranci daurin auren a tsakanin amarya Fatima Sarki Rilwanu da angonta Abdullahi Ibrahim da ya gudana a cikin babban masallacin Juma’a da ke kofar fadar Sarkin. 


Muhimman mutane ne suka halarci daurin auren da suka kunshi har da tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, yayin da shi kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Jodi, kana Kwanturola Janar na hukumar hana Fasa Kwauri, Hamid Ali, sarakuna a ciki da wajen jihar ne suka halarci wannan dauren auren.


Sarkin Lafiya, Alhaji Muhammad Sidi Ibrahim shi ne ya kasance waliyin amarya yayin da shi kuma Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk ya kasance waliykn ango. An kuma daura auren ne kan sadaki naira dubu dari daya.


A jawabinsa na fatan alkairi bayan daurin auren, gwamna Bala Muhammad, ya taya amaren murna tare da musu addu’ar Allah ba su zaman lafiya da zuri’a dayyiba.


Shi kuma Sarkin na Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya mika godiyarsa na ga wadanda suka halarci daurin auren, ya yi fatan Allah bar zumunci. 

Leave a Reply