Uncategorized

Gwamnan Gombe Ya Yi Rashin Kannuwa, Aishatu Yahaya Umaru

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi rashin kannuwa mai suna Hajiya Aishatu Yahaya Umaru.

Hajiya Aishatu ta rasu da safiyar yau Lahadi tana da shekaru 48 a duniya, bayan wani gajeren rashin lafiya da ya sameta.

A wata sanarwar da daraktan yada labarai na gidan gwamantin jihar Gombe Ismaila Uba Misilli ya fitar na cewa, “Inna Lillahi Wa Inna lillahi Rajiun. Daga Allah muke kuma gareshi za mu koma. Iyalan marigayi Alhaji Yahaya Umaru na sanar da rasuwar Hajiya Aishatu Yahaya Umaru wacce ta rasu yau bayan fama da geren rashin lafiya.”

Sanarwar ya ce za a yi jana’izar mamaciyar ne da karfe 1 na ranar yau a asibitin koyarwa ta Gwamnatin tarayya da ke Gombe (FTH).

Sanarwar ta yi addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata kana Allah ya sanya ciki Aljanna Madaukaka.

Leave a Reply