Uncategorized

Gwamnatin Gombe ta raba kwamfitoci da kudade wa ɗalibai ‘yan asalin jihar Gombe masu koyon aikin Lauya da harkokin shari’ah.

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi

Gwamnatin Jihar Gombe ta taimakawa ɗalibai ‘yan asalin Jihar Gombe dake karatun lauya a manyan makaratu daban-daban na faɗin Najeriya da kwamfutocin tafi-da-gidanka (laptops) da kuma tsabar kuɗi miliyan talatin da uku, da ɗari takwas da huɗu da dubu biyar don taimaka musu wajen biyan kudaden karatun su da samun ingantaccen ilimi.

Da yake gabatar da jawabi a zauren taro na Ma’aikatar Shari’a a Gombe, Gwamna jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin da ake buƙata dama tallafi don samun kyakkyawan sakamako da cimma burin da ake buƙata na samar da ingantaccen ilimi da hidima ga al’ummah.

Gwamna Inuwa wanda mataimakin sa Dr Manassah Daniel Jatau ya wakilta, yace samar da kwamfutocin na tafi-da-gidanka da taimakon kudin an yi su ne domin karfafa gwiwar daliban na shari’a su gina kansu ta fuskar ilimi don kimtsa kan su ga ƙwarewa a fannin shari’ah.

Sai ya bukaci wadanda aka tallafawan su yi amfani da na’urori da kudin yadda ya kamata, yana mai cewa ”Gombawa diban fari” (mutanen Gombe a ko yaushe suna kan gaba a cikin duk wata harka mai kyau” da yin kyakkyawan aiki a makarantun su.

Kwamishinan shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin jiha, Zubairu Muhammad Umar, ya shaidawa daliban cewa an shirya taron ne don mika Kwamfutocin na Laptops da taimakon kuɗi Naira dubu 370 ga kowanne dalibi cikin dalibai ‘yan asalin Jihar Gombe su 61, dake karatu a makarantu shida na koyar da shari’ah a Najeriya, yana mai cewa an taimakawa daliban ne don biyan kudaden makaranta yayin da kwamfutocin kuma zasu taimaka musu a harkokin karatun su, yana mai cewa, jimillan taimakon da aka baiwa ɗaliban ya haura Naira miliyan talatin da uku, da ɗari takwas da huɗu da dubu biyar.

Barrister Zubair Umar ya bayyana cewa hakan wani karamci ne ta Gwamnatin Inuwa Yahaya ke jagoranta wajen hidima ga jama’ar jihar, tare da yin kira ga ɗaliban dasu sakawa gwamnatin jihar ta hanyar jajircewa da karatun su da hidimar al’ummar Gombe.

Kwamishinan ya kuma yabawa karamcin Gwamnan ta hanyar taimakon daliban wadanda iyayensu masu karamin karfi ne kuma ba sa iya biyan kuɗin karatunsu, ya kara da cewa duk da cewa ba a nemi su sanya hannu kan wata yarjejeniya ba, gwamnatin tana kyautata zaton daliban za su zama jakadun jihar na gari, kuma su taimaka wajen haɓaka ta a wuraren ayyukan su, musamman ganin cewa kuɗaden na masu biyan haraji ne da suka sha wahala wajen samar dasu.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar, Shugaban kungiyar dalibai lauyoyin na kasa reshen Jihar Gombe, Kwamared Idris Mohammed ya yaba da taimakon da aka ba su, inda ya yi alkawarin tabbatar da yin amfani da kudaden da aka kashe a kansu yadda ya kamata.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa taimaka musu ta hanyar ba su kwamfutocin na tafi-da-gidanka da taimakon kuɗi don haɓaka harkokin su na karatu.

Leave a Reply