Uncategorized

Harin Jirgin Kasan Kaduna: Yadda Wata Fasinja Ta Haihu A Hannun ‘Yan Garkuwa

‘Yan ta’addan da suka kai hari kan Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022 sun fitar da hotunan jaririn da wata daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su ta haifa a inda suka boyesu.

‘Yan ta’addan da ake kyautata zaton mambobin kungiyar Ansaru ne da suka balle daga jikin Boko Haram, sun fitar da hoton sabon jaririn ne a ranar Laraba da yammaci.

Wani makusancin wacce ta haihu a hannun ‘yan garkuwan ya shaida wa majiyarmu cewa ‘yar uwan nasu ta haihu tun a karshen mako.Sai dai ba a kai ga samun hakikanin haihuwar ba har sai da ‘yan ta’addan suka sake hotunan sabon jaririn a ranar Laraba.

Idan za ku iya tunawa ma dai a ranar Talata ‘yan bindigan sun fitar da hotunan mutanen da suke tsare a hannunsu wanda aka tabbatar wata mai juna biyu daga cikinsu ta haihu.

Leave a Reply