Jama’are/Itas Gadau: Ko A Kotun Ma Muke Da Nasara, Insha Allah, Cewar Hon. Kashuri
Daga Mohammed Kaka Misau
Zababben dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Jama’are/Itas Gadau a majalisar wakiltai ta kasa, Hon. Bala Rabilu Kashuri a karkashin Tutar Jamiyyar APC, ya sha alwashin cewa, nasara ta sa ce koda masu adawa sun garzaya kotu don kalubalantar nasararsa.
A cewarsa, al’ummar mazabar sun amince masa lura da kyawawan manufofin da ya zo da su kuma da yardar Allah kotun ma za ta tabbatar masa da nasararsa domin a cewarsa shi ya ci zabe.
Matakin dai na zuwa bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da nasaran cin zabensa.
Da ya ke zantawa da manema labarai a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a kan hanyarsa ta tafiya Umara zuwa kasa mai tsarki, ya ce, abokin takaransa ya kai kara kotu inda yake korafi akan nasaran da ya samu don haka ne ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, “Wannan hidimace ta siyasa ba za ka kayar da mutum ba kuma ka hanashi kuka ba.
“Saboda haka ina amfani da wannan dama na yi kira ga dukkan jama’armu na mazabar Jama’are/Itas Gadau su kwantar da hankalinsu yadda Allah ya ba mu nasara a zaben fidda gwani muka yi nasara kuma muka yi nasara a zaben gama gari (General Election) haka Insha Allah mu ne da nasara a kotun ma Insha Allah.”
Kashuri ya yi kira zuwa ga al’ummar mazabarsa da su yi amfani da wannan dama na watan Ramadan domin dagewa da addu’o’i.
Daga bisani zabebben dan majalisan ya yi godiya wa jama’ar mazabarsa bisa zabinsa da suka yi da ba shi goyon baya da suke ba shi kullum ba dare ba rana yana godiya.