Jam’iyyar YPP Ta Lashe Kujerar Kansila A Bauchi
A ci gaba da ayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da na Kansiloli da ke ci gaba da gudana a jihar Bauchi a ranar Asabar, Samira Shu’aibu Maikano daga jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) daga gundumar Wandi a ƙaramar hukumar Dass ta lashe zaɓen Kansila.
Samira Shu’aibu ta samu ƙuri’u 1610, a yayin da Bashir Abdullahi daga jam’iyyar PDP ya zo na biyu da ƙuri’u 1352 sai Abdulwahab Aliyu daga APC da ƙuri’u 230.
Ana dai cigaba da tattara sakamakon zaben kamar yadda rahotonnin ke zuwa. Sai dai, Wakilinmu ya tabbatar da cewa mafi yawancin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli PDP ce ke lashewa.