Jawabin Tinubu Ya Ingizamu Sai Mun Kara Kwana 10 Kan Zanga-zangar Yunwa – Cewar Masu Zanga-zangar
Masu zanga-zangar neman kawo karshen shugabanci marar alkibla da neman dawo da tallafin mai, sun ce babu komai a cikin jawaban shugaban kasa Bola Tinubu illa ma kara musu haushi kan yunwan da ke damun al’umman kasa.
Comrade Yahaya M Abdullahi, daya daga cikin Jagororin zanga-zangar lumana kuma Shugaban Ƙungiyar Arewa Youth Ambassadors, ya sanar a cikin wata sanarwar da ya fitar cewa, da yiyuwar jawabin Tinubu zai sa su kara kwanaki 10 kan 10 da suka shirya yi tun farko.
Ya ce, “Abun takaici da ƙunci a ce wai shugaban ƙasa ne zai yi irin wannan jawabin ga ƴan ƙasa a wannan halin da ake ciki na yunwa, rashin tsaro, mawuyacin hali, amma shi kawai ƙarfin jawabinsa shi ne a dakatar da zanga-zangar lumana da ake yi.
“A yankinmu na Arewa ana yi wa Uwa fyaɗe a gaban ɗanta, ana yi wa ‘ya Fyaɗe a gaban Ubanta, ana yi wa Matar aure fyaɗe a gaban Mijin ta, amma duka wannan bai dami shugaban ƙasa ba kawai damuwarsa kan Titi da Talakawan da suka zaɓe su suka fito, su na faɗa masa halin da suke ciki.”
Yahaya ya cigaba da cewa: “Ga harajin noma da ake biya da sauran abubuwan, duka a yankin mu na arewa ne fa ake wannan amma ba mu isa mu yi magana ba, a haka zamu ci gaba da zura ido?
“Daga cikin abubuwa 13 babu ko guda ɗaya don amfanar ‘yan ƙasa, ko biya wa masu zanga-zanga bukatarsu domin su koma gida, shi kawai damuwar sa a bar shi ya ci gaba da gallaza wa mutane kada wani ya masa magana, hakan ne ya sa a baya ya gayyaci Malamai da sauran su domin ganawa dasu akan su kwantar da hankalin jama’a.”
“Batun dakatar da zanga-zangar lumana da shugaban kasa, Tinubu ya ce a yi tamkar fito na fito ne da tsarin dimokiradiyya da muke tunkaho da ita a yanzu, bugu da kari cikin hujjojinmu na zanga-zangar lumana har da koyi da shi, domin ya fi kowa iya shirya zanga-zanga a Nijeriya.”
“Ya zama wajibi a biya mana bukatunmu a matsayin mu na yan kasa, domin kuwa matukar Gwamnati ba za ta biya bukatun ‘yan kasar da suka sadaukar suka sha rana suka zaɓe ta ba to ka ga bata da amfani kenan, a yanzu muna iya cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta da amfani ga dukkan talakawan Nijeriya, saboda haka su na iya sauka ko kuma su mana abunda muke bukata.”
“Daga ƙarshe, muna kira ga ‘yan Nijeriya, musamman Matasa Zanga-zanga ba gudu ba ja da baya, in mun kammala kwanaki 10 zamu sake ƙara wasu kwanakin goma har sai an biya mana bukatun mu, zanga-zanga ta lumana ba tashin hankali ba ƙona kayan kowa, dama in ka ga anyi tashin hankali to jami’an tsaro su suka zo suka haifar mun saba gani a baya kuma yanzu ma muna gani.”