Hausa

Allah Ya Yi Rasuwa Wa ‘Yar Uwan Mawallafin BausheTimes

Inna lillahi wa inna illahir raji’un.

Allah ya yi rasuwa wa babbar Yayar mawallafin jaridar yanar gizo ta BAUSHETIMES Malam Mohammed Kaka, wato Malama Balkisu Abubakar.

Ta rasu ne a ciren daren ranar Lahadi ta na kwance cikin barci kuma rasuwar farat daya (Fuju’a) ta yi.

Za a yi jana’izarta da karfe 10am na ranar Lahadi 21/April/2024 a babban masallacin kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Misau, Bauchi.

Ana gayyatar al’umma zuwa mata sallar jana’iza da kaita makwancinta na dindindin. Muna kuma roka mata addu’ar neman gafara a wajenku. Allah ya jikanta ya gafarta mata kura-kuranta kuma ya sanyata cikin aljanah madaukakiya.

Leave a Reply