Kotu Ta Hana Belin Abduljabbar Yayin Da Sabbin Lauyoyi Suka Bayyana Don Cigaba Da Kare Shi
Daga Aliyu Samba
A yau ne kotun shari’ar Muslunci ta Alƙali Ibrahim Sarki Yola dake zama a kofar kudu ta cigaba da sauraren shari’ar Malam Abdujabbar Kabara da Gwamnatin Kano.
A yayin zaman na yau, sababbin lawyoyin sun bayyana a kotu a matsayin lawyoyin Malam Abduljabbar, kuma sun nemi a basu kwafin shari’ar dan su nazarce ta, sannan suna neman a basu belin Malamin saboda dalilai kamar haka;
Waɗanda suke ƙarƙashin Malam Abdujabbar suna shan wahala sosai duba da halin da ake ciki, kuma wanda ake ƙarar mutum ne mai mutunci kuma sananne a cikin al’umma. Sannan ya ƙara da cewa bada shi beli zai taimaka wajen bawa wanda ake ƙara cikakkiyar damar tattara hujjojin da zai gabatar wa kotu.
Alƙali ya nemi jin ta bakin lawyoyin wanda ke kara, inda suka yi suka akan neman belin wanda ake ƙara.
Lawyan wanda ke ƙara ya ce da kotu, ”aikin Lawya shine ya ja Shari’a ya faɗi Sashe, ya fassara shi da ma’anar sa. Sheda ne zai faɗi halin da na kasan wanda ake ƙara suke ciki ba wai Lawya ba”
Ya ƙara da cewa ”Tun daga lawyoyin baya da suka janye daga kare wanda ake ƙara, da su waɗannan na yanzu, babu wanda a cikin su ya ce da kotu an taba hana shi ganin wanda suke karewa, ko an hana shi ya shirya hujjojin sa.
Sannan ya kara da cewa indai akwai tuhuma irin wannan babba a gaban kotu kuma an fara sauraren shari’ar, ba a bada shi beli dogaro da Sashe na 171 ACJN, karamin sashe na 1.
Lawyan wanda ke ƙara ya cigaba da cewa wannan roƙo da Lawyoyin wanda ake ƙara sukai bashi da madogara da zata talafe shi daga doka, domin a cikin sharudan bada beli a tuhuma babba irin wannan, babu batun cewa (Idan na ƙasan wanda ake ƙara suna shan wahala a bada belin sa).
Alƙali ya ce da lawyoyin wanda ake ƙara ko suna da suka ko martani da nassi ko doka, lawyan wanda ake ƙara yace ”Mudai mun gabatar da rokon mu, mun bawa kotu ta fadi ra’ayin ta”
Alƙali bayan sauraren duka ɓangarori biyun tare da nazartar rokon bada belin Malam Abdujabbar, da sukar da lawyoyin gwamnatin sukai, ya ce ”Wajibi ne Alƙali ya dogara da abinda doka da nassi suka tabbatar.
”tuhumar da akewa wanda ake ƙara babban laifi ne da ake hukuncin kisa idan aka tabbatar da anyi laifin, doka ta ACJN ta lissafo laifukan da ake bada beli tare da sharaɗin bada beli, saidai babu inda doka tace dan na ƙasan wanda ake ƙara suna wahala a bada belin sa” inji Alƙali
Ya ƙara da cewa “Ni akan kaina bani da hujjar yin abinda baya cikin doka ko nassi, domin doka ce ta dora Ni a matsayin alƙali”
Alƙalin ya jaddada cewa zai bawa wanda Malam Abdujabbar damar kare kansa, kuma baza su hana a kai masa littafai koda kuwa sun kai cikin mota guda tunda magana ce ta ilimi, kuma baza su hana lawyoyin sa damar zuwa wajensa suyi tattaunar ilimi ba akan shari’ar.
”Wajibin alƙali ne ya tsare mutunci da lafiyar wanda ake ƙara, duba da yanda garin nan yake yanzu, ba daidai bane na bada belin wanda ake ƙara saboda saɓanin dake tsakanin sa da al’ummar gari” inji alƙali.
Alƙalin ya ƙara da cewa ba wai ya hana beli bane kwata kwata, idan hali yayi ya ga raunin hujjojin shedu, zai iya bada belin Malam Abdujabbar. Ya bada Umarnin lawyoyin Malam Abduljabbar suje ofishin C.R.O a basu kwafin shari’ar.
Alƙali ya ɗage Shari’ar zuwa 14 ga watan Oktoba,2021 dan cigaba da Shari’a kuma yayi umarnin wadanda suke ƙar