FEATURED

KADDAMAR DA KANSILOLI MASU OFFICE DA SHUWAGABANNIN KOMITOCIN GUDANARWA NA MISAU LGA.

By Mohammed Kaka Misau.

Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, Minority leader ya halatci zama na musamman a karamar Misau don kaddamar da kansiloli masu office da nada Shuwagabannin komitocin gudanarwa daban – daban wanda kansilolin ke jagoranta.

Hon. Bakoji Aliyu Bobbo ya shawarci kansilolin da su kasance masu biyayya ga shugabanci da jajircewa gurin runguman hidimar al’ummar da suke wakilta ba dare – ba – rana.

Minority leader Ya yabawa shugaban karamar hukumar Misau, Rt. Hon. Abubakar Ahmed Garkuwan Misau bisa yadda yake tafiyar da harkan Misau L. G. a cikin sanin makamar aiki da iya zama da ma’aikatan gomnati da yan siyasa a tafiyar da harkar shugabancin sa.

Hon. Abubakar Ahmed Garkuwan Misau a jawaben sa, ya yabawa Hon. Bakoji Aliyu Bobbo bisa wakilci mai inganci da ayyukan alkhairi da yake gudanarwa a yankin chiroma. Ya bayyana minority leader a matsayin jajircecce mai kokari da himma gurin taimakon al’ummar sa da zama cikin al’ummar da yake wakilta don sauraron koken su ba dare – ba – rana.

Wadanda suka halarci wannan zama sun hada da Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, Minority leader, Hon. Abubakar Ahmed Garkuwan Misau, chairman Misau LGA, Hon. Salisu Dando, Deputy Chairman Misau LGA, Hon. Abdu Haruna, Chairman PDP Misau LGA, Alh. Yarima Sa’in Misau, Alh. Babangida Babayo, Katukan Misau, Alh. Babangida Bangarati, da sauran su.

Allah ya taya su riko, ya musu jagoranci a wadannan shugabanci.

Amiin!

Babangida Mohammed
P. A. to Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, Minority Leader BAHA
21st December, 2020

Leave a Reply