Uncategorized

Kwamitin APC Ya Hana ‘Yan Takara 10 Shiga Zaben Neman Tikitin Shugaban Kasa

Kwamitin tantance ‘yan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya haramta wa ‘yan takara 10 daga cikin 23 da suke neman tikitin tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023 damar shiga a dama da su a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Shugaban kwamitin kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Chief John Odigie-Oyegun, shi ne ya shaida hakan a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Juma’a sa’ilin da kwamitin ke ke gabatar da rahoton aikinsa.

Kan hakan, ‘yan takara 13 ne kawai za su shiga a dama da su a zaben fitar da gwani na jam’iyyar da ke tafe.

Kodayake, Odigie-Oyegun, bai ayyana sunan kowa daga cikin wadanda suka hana musu damar shiga zaben ba, ya ce, jam’iyyar za ta yi abun da ya dace.

Ya ce, kwamitin ya yi la’akari da matasa da ire-iren su da suke shiga a dama da su a takarar a yayin gudanar da aikin nasu a kwamitance.

Odigie-Oyegun sannan kuma ya tabbatar da cewa, kwamitin nasu bai tantance tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ba, saba’in jita-jitan da ake ta yadawa na cewa Jonathan na daga cikin jerin ‘yan takara.

Leave a Reply