Uncategorized

Magoya Bayan Atiku Ga Wike: Burgarka Ba Za Ta Tsoratamu Ba

Daga Mohammed Kaka Misau

Mambobin kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, sun sha alwashin cewa,
burga da kumfar bakin gwamna Nyesom Ezenwo Wike ba za su tsoratasu ko firgita su ba.

Sun shelanta goyon bayansu dari bisa dari ga dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, suka ce, duk da barazanar umarni kamu da gwamnan ke musu ba za su bar so da kaunar Atiku ba.

Darakta Janar na kwamitin yakin zaben a jihar kuma tsohon ministan Sufuri, Dakta Abiye Sekibo, shi ne ya shaida hakan a garin Fatakwal yayin ganawa da kungiyar Atiku Democratic Movement da Concerned Ogoni PDP Elders’ Council.

Sekibo ya bukaci masu zabe da su yi watsi da salon yaki da Atiku da Wike ke yi, tare da tabbatar da cewa sun zabi Atiku Abubakar a yayin babban zaben 2023.

“Atiku na da dumbin masoya da magoya baya a Ribas, kuma har yanzu suna nan daram a yadda suke. Sun yayyaga hotunan Atiku, amma muna nan daram-dam kan gaskiya.”

Shi kuma a bangarensa, mambar kwamitin yakin zaben, Sir Celestine Omehia, ya ce, rikicin cikin gida na jam’iyyar ya kawo karshen don haka sun dukufa wajen ganin PDP ta samu nasara.

Omehia ya ce: “A kowace gida akwai rashin fahimta, dawowa ku hada kanku bayan wannan rashin jituwar shi ne abun nema.”

Leave a Reply