Mata Na Da Rawar Da Za Su Taka Wajen Cigaban Al’umma Idan Aka Ba Su Dama, Inji Maryam Abacha
Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, wato Hajiya (Dr) Maryam Abacha ta ja hankalin al’umma musamman mazaje da su rika bai wa mata dukkanin wata dama da ‘yanci na neman ilimi da aiki ko sana’a domin ci gaban al’umma baki daya.
Dr Maryam Abacha ta bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin da take ganawa da manema labarai a gidanta dake birnin Tarayya Abuja.
Hajiya Maryam ta ce mata suna da tasirin gaske wajen gina ingantacciyar al’umma, domin su ke tarbiyyar al’umma, inda ta yi amfani da wannan dama wajen kira na musamman ga mazaje da su rika bai wa matansu dama ta neman ilimi da aiki ko sana’a.
Dr Maryam ta ce maza musamman a arewacin Nijeriya ba su cika taimakawa matansu wajen cimma burinsu ba, wanda ta ce hakan na matukar dakile ci gaban yankin. Sai dai ta ja hankalin matan da cewa duk wacce ta samu dama to ta zama mai kare mutucinta, domin a cewarta; “kare mutunci na da matukar amfani”.
Har wala yau a wani bangare na bayaninta, ta yi tilawar yadda ta rika bai wa mijinta shawarwari wadanda a karshe suka taimaki al’umma da kasarnan. A nan ne ta jawo hankalin mata da cewa; akwai bukatar su rika taimakon mazajensu ta hanyar ba su shawarwari da bayanai da za su taimakawa mazajensu da al’umma baki daya.
Sannan ta ja hankalin mazan da cewa yakamata a bangarensu su rika jin shawarwarin matansu, wanda ta ce idan miji na sauraren shawarwarin matarsa, tabbas zai amfane shi; “na sha bai wa maigida shawara, kuma ya dauka ya amfanar da kasa”, ta jaddada. Ta kara da cewa; “yana da kyau mace ta shiga aikin mijinta domin kawo gyara wanda zai amfani al’umma”, ta lurantar.
Sannan ta janyo hankalin al’umma cewa duk wanda ya samu kansa a wani matsayi ko mukami, to ya tabbata ya hidimtawa al’umma kuma ka da ka kasance mai danne na kasa da kai, domin a cewarta rayuwa na sauyawa. Inda ta ce; “Rayuwa yana da kyau idan ka samu dama; kudi ko mulki, ka yi adalci, kirki da kuma gaskiya. Rayuwa wucewa take yi”.
Har wala yau ta shaidawa ‘yan jaridar cewa; duk wani aiki da mutum ya kuduri aniyarsa ya yi shi da kyakkyawan niyya, “tabbas Allah zai taimake shi”, inji ta.
Sannan ta ja hankalin mata da su rika bibiyar tarihin wadanda suka gabace su domin fahimtar kura-kuran da suka yi domin su kuma su dauki darasi. Ta ce akwai bukatar mata su rika daukar darussa na rayuwa.
Hajiya (Dr) Maryam Abacha har wala yau a bayaninta ta zayyano irin ci gaban da ta samar a lokacin da ta rike shugabancin kungiyar matan ofisoshi sojoji wato NAOWA da kuma zuwa lokacin da ta zama Uwargidan shugaban kasa. A yayin da ta rike shugabancin NAOWA, ta samar da dimbin shirye-shirye na tallafawa sojoji da matan sojoji ta hanyar ilmantar da ‘ya’yansu, koyawa mata sana’o’i da kuma ba su tallafi. Baya ga haka, ta kafa kungiyar hadaka ta matan sojoji da ‘yan sanda wato JOFOPOWOCCO wacce daga baya aka sauya wa kungiyar suna zuwa DEPOWA, wato kungiyar matan hafsoshin tsaro da ‘yan sanda domin kyautata alakar dake tsakanin fadar shugaban kasa da kuma wadannan rassan tsaro.
Daga cikin dimbin nasarorin da ta samarwa da Nijeriya a yayin da take rike ofishin Uwargidan shugaban kasa, sun hada da; shirin tallafawa iyali; shiri da ke tallafawa iyali a bangaren ilimi, lafiya, noma da kiwo, samar da kudaden shiga, tallafawa gajiyayyu da sauran su. Sannan ta samar da shirin ci gaban tattalin arzikin iyali, shirin allurar rigakafi ta kasa, shiriin tallafawa masu bukatar shigar da kara gaban shari’a, asibitin kasa na mata da kananan yara, bayar da gudummawa ga fadar shugaban kasa, shirin gwamnati, samar da ofishin tuntuba na tsoffin shugaban kasa da iyalinsu da sauran su.
Baya ga haka, a bangaren lafiya ta kirkiro shirin yakar cutar kanjamau da kuma na allurar rigakafi ga kananan yara. Wanda shiri ne da aka bullo da shi domin yakar cututtuka shida da suka fi addabar yara a wancan lokacin. Saboda irin wannan gudummawar da ta bayar hukumar lafiya ta duniya ta nada ta a matsayin Jakadiyyar kawar da cutar foliyo a Afrika.
Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Maryam Abacha bisa shawararta aka samar da ma’aikatar lura da harkokin mata da ci gaban zamantakewa a 1995.