Uncategorized

Buhari Ya Kafa Kwamitin Mika Mulki Yayin Da May 29 Ke Karatowa

  • Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Zartaswa Ta 14 Don Tsara Sauyin Gwamnati

Daga Khalid Idris Doya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da kafa kwamitin mika mulki na shugaban kasa da za su tsara yadda za mika ragamar mulki ga sabuwar gwamnati da Allah zai kawo a 2023.

Mambobin Majalisar shirye-shiryen mika mulkin sun kunshi: Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a matsayin shugaba; shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya, babban Lauyan kasa kuma babban Sakataren ma’aikatar shari’a a matsayin mambobi.

Sauran sun hada manyan sakatarorin ma’aikatar tsaro, ma’aikatar cikin gida, ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, ma’aikatar kula da harkokin waje, yada labarai, hukumar babbar birnin tarayya Abuja (FCTA) da na ma’aikatar ayyuka na musamman da kula da kula da lamura tsakanin gwamnatoci.

Sauran sun hada da ofishin harkokin Majalisa, ofishin sakataren Gwamnatin tarayya (OSGF), babban ofishin ayyuka a OSGF, ofishin kula da harkokin tattalin arziki da na harkokin siyasa na OSGF, fadar shugaban kasar, babban hadimin shugaban kasa a bangaren tsaro, shugaban hafsin sojoji, Sufeton Janar na hukumar ‘yansandan Nijeriya, darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa, darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya (SSS), babban rijistaran kotun koli; da mutum biyu wakilai daga shugaban kasan da Allah bai wa nasara (Wanda jama’an kasa suka zaba a 2023).

A cewar wata sanarwar da mai magana da yawun sakataren Gwamnatin tarayya ya fitar, ya ce, za a kaddamar da kwamitin ne a ranar Talata 14 ga watan Fabrairun 2023 da sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha zai jagoranta.

Kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarraba hannu kan dokar zartaswa mai lamba 14 na 2023 da zai tsani tare da jagoranci tsara canjin shugaban kasa.

Babban abin da ke kunshe cikin Dokar Zartaswa ta Shugaban Kasa mai lamba 14 ta 2023 ita ce kafa tsarin shari’a da zai ba da damar mika mulki ba tare da wata matsala ba daga wannan gwamnatin ta Shugaban kasa zuwa wata da ke zuwa da zai gaji shugaba Muhammadu Buhari nan da watanni kalilan masu zuwa.

Leave a Reply