Uncategorized

Misau 2023: Wani Jigon PDP Ya Kimtsa Ficewa Daga Jam’iyyar

Daga: Mohammed Kaka Misau

A daidai lokacin da muke fuskantar hada-hadar zaben 2023, jaridar yanar gizo ta BausheTimes ta jiyo daga wata majiya cewa wani jigo Kuma kusa a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Misau na Shirin ficewa daga jam’iyyar.

Tunin majiyar ta nuna cewa jigon da muka sakaye sunansa don wasu dalilai zuwa yanzu na kan tattaunawa da magoya bayansa da masoyansa domin matakin da za su dauka na gaba bayan ficewa daga PDP din tare da zabin wata jam’iyyar ta daban ko kuma yin muhawara don cigaba da zama ita PDP din.

A wata majiya kuma jigon siyasan ya gana da wani na gaba gaba a tafiyar Atiku Abubakar, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, dangane da batun ficewarsa.

Kana ya samu tabbaci daga wajen jigon ma cewa ya yi abin da ya ga ya dace masa.

Cikakken yadda ta kaya na zuwa daga baya:

Leave a Reply