Hausa

Ni Ne Abokin Karawarka A Siyasa Ba Tinubu Ba – Sanata Buba Ga Gwamnan Bauchi

Daga Khalid Idris Doya          

Sanata Mai Wakiltar Mazabar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya ce, soka da caccakar da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya yi wa shugaban kasa Bola Tinubu kan matsin rayuwa da ake ciki, ya yi ne kawai domin wawaitar da hankulan jama’an jihar daga maƙuden biliyoyin da tulin tirelolin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta turo jihar.

Ya kuma ce, gwamnatin jihar ta PDP ita ce ta kakaba wa jama’an jihar yunwa da matsin rayuwa domin gwamnatin tarayya ta bayar da tirelolin shinkafa, taki, dawa domin rabar wa jama’a kyauta, ya zargi gwamnatin jihar da cewa ba ta rabar ba.

Sanatan wanda ke jawabi a ƙarshen mako yayin bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe da miƙa wa ‘yan takara tuta na zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 20 da kansiloli 323 da zai gudana a jihar Bauchi ranar Asabar 17 ga watan Agusta.

Buba ya ce: “Talaucin da ake ta kuka a jihar Bauchi, gwamnatin jihar ce ta assasa mana shi ne. Bar na gaya mana, ni sanata ne da ke wakiltar Bauchi ta Kudu, duk abun da ake damawa a Abuja a idona ake yi. Ina gaya muku daga 2023 zuwa Janairu jihar Bauchi ta karɓi sama da naira biliyan 144 daga asusun hadaka na tarayya (FAAC), ina waɗannan kuɗaɗen suke? ya fito ya karyata abun da na fada.

“Daga watan 1 zuwa yau, jihar Bauchi ta karɓi sama da naira biliyan 47, kuma zuwa ƙarshen shekarar nan za ta karɓi kuɗi kimanin naira biliyan 195. Amma yaushe zai zo ya tsaya ya yi ƙarya, ya ce wai gwamnatin APC ta kawo yunwa, balle kai ne kake riƙe da lalitar jihar Bauchi me kake yi wajen kawo sauyi a cikin tsanani da ake ciki?.

“Al’umman Bauchi su na kallonka kowa yana kallonka. Ina tabbatar muku cewa, yanzu kamar wata shida da suka wuce akwai tirololi na Dawa 70 da aka bayar a kawo wa jihar Bauchi, jihar Bauchi an ba ku? ina ya kai su?. ku tamabaye.

“Akwai Taki Tireloli 70 da aka bayar a kawo Bauchi kyauta amma yanzu ya zo yana sayar muku a kan naira dubu 50,000. Kwanan nan an bayar da tirelolin Shinkafa 20 don a kawo wa ‘yan jihar Bauchi, ya ba ku?

“To, waye ya riƙe kuɗaɗen da kayan abinci da ake kawowa daga gwamantin tarayya?

“Kuma kowa ya sani ya je ya ciwo bashi na sama da naira biliyan 300 kuma harƙar hanya ko kwangilar haya shi ya kawo kamfaninsa ne.”

Ya ƙara da cewa, “Mu muna zaman lafiya da kai ba mu nemeka da faɗa ba, kai ka tsokano mu ka zage mu, shi ya sa na ce yau za mu biyaka bashi guda ɗaya. Za mu saurareka mu ji amsarka, muna da dozin da za mu amayar wa mutanen jihar Bauchi.”

Shehu Buba da yake magana kan zaɓen, ya tabbatar wa jama’a cewa a shirye APC take, har ma ya bada tabbacin cewa su ne za su lashe zaɓen shugabannin da na kansiloli muddin aka yi adalci.

Ya nemi al’umman jihar da su fito kansu da ƙwarƙwatarsu da su zaɓi APC domin cetosu daga matsin rayuwa da suke ciki, kana ya kuma ce za su kwace mulkin jihar daga hannun PDP a 2027.

Ya ce, “Muna ƙalubalantar hukumar zaɓe ta jiha da ta fito da gudanar da zaɓe na adalci. Mu kuma a shirye muke, ana ta tsorata mutane cewa ba za a shiga zaɓe ba, za a rubuta kamar yadda aka yi a baya, to mu muka ce za mu shiga zaɓen nan kuma da ikon Allah za mu ci zaɓen nan. Abun da muke nema hukumar zaɓe ta kai kayan zaɓe kowani rumfa, in aka yi zaɓe na adalci ina tabbatar muku ko kujera ɗaya PDP ba za ta ci ba.”

Shi ma a nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Muhammad Hassan Tilde, ya gargaɗi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi kan yin maguɗi ko taimaka wa PDP da gwamnatin jihar su yi musu maguɗi, ya ce, a shirye suke su kara da kowace jam’iyya kuma su yi nasara.

Ya nemi wakilansu da masu sanya ido da su gudanar da ayyukansu yadda ya dace domin daƙile abun da ya kira shirin musu maguɗi.

Leave a Reply