Uncategorized

Sallah: Gwamnan Gombe Ya Gwangwaje Mata Da Matasa Da Miliyan 114



Jam’iyyar APC ta Jihar Gombe ta bayyana farin ciki ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa karimcinsa na fitar da kudi har naira miliyan 114 ga matasa da mata a fadin gundumomi 114 na jihar domin su samu damar gudanar da bukukuwan babbar sallar nishadi.


Shugaban jam’iyyar na jihar Gombe, Mista Nitte Amangal ne ya yi wannan yabon a sakatariyar jam’iyyar ta jihar yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro.


Ya ce, hakan na daga cikin kudurin Gwamna Inuwa na samar da tallafi ga talakawa a lokutan bukata kamar bukukuwan sallah. Ya jaddada cewa wannan karimcin na musamman ne ga matasa da mata ne kadai, yayin da na barka da sallah na nan tafe.


Mista Nitte Amangal ya yi imanin cewa matakin zai saukaka wahalhalun da mutane da dama ke fuskanta yayin bukukuwan, musamman matasa da mata.


“Lokacin bukukuwa musamman na babbar sallah ana bukatar sadaukar da dabbobi kuma ba shakka wannan karimcin da gwamna ya yi zai taimaka sosai wajen tallafawa wadanda suka ci gajiya wajen samun abin yanka”.


Mista Amangal ya yi alkawarin raba kudaden cikin gaskiya da  adalci.


Da yake karin haske kan tsarin rabon kudaden, Sakataren Yada Labaran jam’iyyar Moses Kyari, ya shaidawa manema labarai cewa jam’iyyar za ta bi umarnin gwamnan wajen zabo mutane 100 daga kowace gunduma cikin gundumomi 114 dake fadin Jihar domin rabawa ga wadanda aka yaara a dukkan matakai.


Ya bayyana cewa Gwamnan ya umurci jam’iyyar ta zabo mutane dari daga kowace gunduma cikin gundumomi 114 dake fadin jihar, amma banda shugabannin jam’iyyar a wannan karimci.


Kyari ya yi kira ga al’ummar Jihar Gombe su hada kai da Gwamna Inuwa Yahaya da gwamnatin APC don ci gaba da sharbar romon demokradiyya.

Leave a Reply