Uncategorized

Sanarwar Daurin Aure

Iyalen Maigirma Danmasanin Dambam Alh Makama Mohammed dake aiki a Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital Bauchi, Suna Farincikin Gaiyatar ‘Yan Uwa Da Abokan Arziki Zuwa Wajen Shaida Daurin Auren Diyarsu Mai Al’barka,

Amina Mohammed Makama Dambam wace akema Laqabi da Adda Yusurah ‘daliba a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi

Da Angonta Muhammad Ukasha Abdullahi

Dayardar Allah Kafin ranar daurin Aure za’a fara gudanar da Walimar Amarya A Ranar Juma’a 20/1/2023. Wacce Dr. Zuhuriyya Usman Sulaiman zata isar da sako na musamman da misalin Karfe 4:00 Na Yamma, a dakin taro na tunawa da Marigayi Sheik Jafar Mahmood Adam dake cikin Masallacin Gwallaga a Jihar Bauchi.

A Ranar Asabat 21/1/2023 za’a daura Aure da karfe 11 na safe A Babban Masallacin Juma’a dake Fadar Maigirma Sarkin Dambam Cikin garin Dambam a Jihar Bauchin Nigeria

Allah Yabada Ikon Halarta Amin

Sanarwa Daga Wakilin Tarihin Dambam Comr. Alh Musa Mohammed Dambam Sarkin Ayyukan HAFYDOF NIGERIA, Amadadin Iyalan Gidan Maigirma Danmasani Dambam.

4 thoughts on “Sanarwar Daurin Aure

Leave a Reply