Sanatan Bauchi Ta Kudu Ya Bada Tallafin Miliyan 50 Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Borno
Daga Khalid Idris Doya
Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya bayar da tallafin Naira miliyan 50 domin a rabar ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.
Buba ya miƙa kyautar ne a lokacin da ya ziyarci Maiduguri domin jajanta wa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da al’ummar jihar bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta yi mummunar ta’adi a jihar.
A wata sanarwar mai ɗauke da sanya hannun hadimin Sanatan a ɓangaren yaɗa labarai, Sulaiman Lalaye wanda ya rabar a Bauchi jiya, Buba ya nuna takaicinsa kan irin ɓarnar da ruwan ya yi, sai ya kuma jinjina wa irin ɗaukan matakan gaggawa da gwamnatin jihar Borno ta yi wajen samar da agajin gaggawa ga waɗanda lamarin ya shafa kai tsaye.
Sanata Buba wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro da leƙen asiri na ƙasa na majalisar dattaɓai, ya kuma yaba ga irin matakin hanzari da gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen samar da tallafi da taimako ga waɗanda lamarin ya shafa.
Kazalika, ya yi ƙira ga masu hannu da shuni da sauran ƙungiyoyin agaji da su bayar da nasu gudunmawar domin taimaka ma jama’an da ambaliyar ta lalata wa ƙadarori da tursasa musu ƙaura daga muhallansu.
Da ya ke jajantawan, ya kuma yi addu’ar Allah kawo sauƙin halin da ake ciki a Borno da kuma addu’ar Allah jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar, tare da addu’ar Allah bai ma waɗanda suka jikkata lafiya.
Shi kuma a nasa ɓangaren, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gode wa Sanatan bisa tallafin da ya kawo da tattakin da ya yi domin jajanta musu a irin wannan mawuyacin hali da suke ciki. Ya tabbatar da cewa tallafin za a rabar da su bisa gaskiya da adalci.