Uncategorized

Shirin Sallah: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ga Tawagar Shugaban Kasa A Katsina

Daga Idris Khalid

Fadar shugaban kasa ta nuna takaici da rashin jin dadi da barin wutar da wasu ‘yan bindiga dadi suka yi ga tawagar motocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wadanda suke kan gaba (advance team) da suka kunshi jami’an tsaro, masu tsare-tsare da shirya wurare, gami da tawagar ‘yan jarida a kusa da Dutsinma ta jihar Katsina a daidai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura domin jiran karasowar Shugaba Buhari don yi masa rakiyar hutun sallah a mahaifarsa.

A cewar sanarwar da Mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce, maharan sun bude wuta ga tawagar motocin daga inda suka yi kwantan bauna, amma a cewarsa sun fuskanci tirjiya da maida musu martani daga jaruman Sojoji, ‘yan Sanda da jami’an DSS da suke cikin tawagar.

Ya ce, yanzu haka mutum biyu daga cikin tawagar farko-farko na shugaban kasan suna amsar kulawar jami’an lafiya sakamakon ‘yan kananan raunuka da suka samu sakamakon harin.

Sanarwar ta ce, dukkanin sauran jami’an tsaro da ‘yan tawagar, ma’aikata da motocin dukka sun Isa cikin Daura mahaifar Shugaban kasa lafiya.

Leave a Reply