Uncategorized

Shugaban APC, Adamu Ya Nuna Damuwa Kan Ficewa Da Wasu Sanatoci Ke Yi Daga Jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna damuwarsa dangane da yawaitar ficewar da Sanatoci ke yi daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyun adawa.

Adamu wanda ke ganawa da ‘yan jarida a ranar Laraba bayan kammala ganawar sirri da suka yi da sanatocin jam’iyyar APC a shalkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Duk da nuna damuwarsa da ficewar tasu, ya bugi kirji ya ce, hakan ba zai shafi wani tasirin jam’iyyar ba.

A cewar shugaban, yawaitar sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wancan, ya saba faruwa a duk kakar siyasa domin wadanda suka ji basu gamsu da sakamakon zaben cikin gida na jam’iyyar su ba, sukan kwashi jiki zuwa wasu jam’iyyun domin sake gwada sa’arsu.

Adamu wanda ke martanin bayan ficewar wasu Sanatoci daga jam’iyyar ‘yan kwanaki kalilan.

A ranar Talata sanatoci uku sun fita daga APC tare da shiga jam’iyyar PDP da NNPP.

Sanatocin sun hada da Ahmed Babba Kaita, da ke wakiltar mazabar Katsina ta Arewa, Sanata Francis Alimikhena, Mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa da suka koma jam’iyyar PDP, sai kuma Lawal Yahaya Gumau, (Bauchi ta Kudu) ya koma jam’iyyar NNPP mai alamar kwando da kayan marmari.

Har-ila-yau, Sanata Halliru Dauda Jika, da ke wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya, ya fita daga APC tare da shiga NNPP.

Sai dai wakilinmu ya labarto cewa daga cikinsu da dama sun shiga zabukan fitar da gwani a APC ne kan kujeru daban-daban amma da suka fadi ne sai suka dauki matakin ficewa daga cikinta.

Leave a Reply