Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Ya Taya Sultan Sa’ad Murnar Cika Shekaru 67
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 CFR, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA) murnar cikarsa shekaru 67 a duniya a ranar Alhamis.
Gwamna Inuwa ya bayyana Sarkin Musulmi Sa’ad a matsayin ginshikin zaman lafiya da hadin kai, wadda matsayinsa na jagora ga Musulmi a fadin Nijeriya ya samar da zaman lafiya marar misaltuwa a tsakanin al’ummar Musulmi dama sauran abokan zamansu, tare da amfanar rayuwar mutane da dama.
A sanarwar da hadiminsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Inuwa ya ce sadaukarwar da Sarkin Musulmin ke yi wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da al’ummar kasa da shugabanninta kan samar da ingantaccen shugabanci na gari.
“A matsayinsa na jagora mai kula da harkokin addini da al’adunmu na gado, mai alfarman ya jajirce wajen ganin an tabbatar da hadin kai da hakuri da juna. Kokarinsa ya taimaka wajen karfafa hadin kai da fahimtar juna tsakanin addinai da wanzar da zaman lafiya, tare da karfafa ginshikin gina al’ummarmu”.
Shugaban kungiyar Gwamnonin na Arewa ya bukaci Mai Alfarman ya ci gaba da amfani da girman sarauta da tasirinsa wajen inganta zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai ma’ana, ba kawai a kasar Sokoto kadai ba, har ma da Nijeriya da sauran kasashe.
Sai ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya karawa Mai alfarma Sarkin Musulmin shekaru masu yawa da koshin lafiya don ci gaba da ayyukan da yake yiwa al’umma da kasa baki daya.