Uncategorized

TATTAUNAWA TA MUSAMMAN: Ranar Zabe Kawai Al’ummar Bauchi Ke Jira Su Zabi Air Mashal A Matsayin Gwamnansu, In Ji Kwamared Sabo

Duk Shika-shikan Fadin Gwamnatin Bala Muhammad A Bauchi Sun Bayyana
APC Ta Kammala Shirin Kwace Mulki A Jihar Bauchi, Cewar Kwamared Sabo

KWAMARED SABO MUHAMMD jigo ne a jam’iyyar APC kuma fitaccen dan gwagwarmayar siyasa a jihar Bauchi wanda ya riqe mukamai daban-daban. A hirarsa da KHALID IDRIS DOYA ya bayyana cewar dukkanin harsashen faduwar gwamnatin Bala Muhammad a jihar sun bayyana, inda ya nuna cewa al’ummar jihar sun gama zaman shirin zabar Air Mashal Sadik Baba Abubakar na jam’iyyar APC a 2023 a matsayin sabon gwamnansu. Ya kuma tabo muhimman batutuwa da suka shafi siyasar jihar Bauchi ga hirar kamar yadda aka yi ta:


A matsayinka na dan jam’iyyar APC kuma jigo a cikinta ya kake harsashen babban zaben 2023 a jihar Bauchi?


Bismillahir rahmanin Rahim. Idan abun da muke ji muke sauraro kuma muke fahimta kuma muke tsinowa daga harsashen dimbin masu zabe ko masu kuri’a a jihar Bauchi to ina son na tabbatar wa al’umma cewa da izinin Allah da yardarsa, Ambasada Sadik Baba Abubakar gwamnan jihar Bauchi ne mai jiran gado.


Meye dalilinka na fadin hakan?


Dalilina shi ne, na farko shi gwamna mai ci Bala Muhammad Kauran Bauchi ya kada gwamna ne mai ci na jam’iyyar APC a 2019 kuma jihar da APCn da take da komai a wancan lokacin, to amma sabili da kura-kurai da aka samu ya sa mutanen Bauchi suka canza da shi bisa dogara da alkawuran da ya yi musu, musamman yadda ya nuna damuwarsa a kan yadda aka yi rikon sakainan-kashi da maganar albashi da rashin biyan kudin kammala aiki ‘giratuti’ da rashin biyan kudin hutu da kuma rashin yi wa ma’aikata karin girma da kuma yanayin rashin aiki marar kyau, da kuma yadda ya ce an sanya jihar Bauchi cikin fatara musamman a bangaren kasuwanci, rashin samar da aikin yi da walwala da kuma rashin tausayawa mutane masu mutunci da kima irin sarakunanmu na gargajiya bihasalima har suka yi alkawarin cewa za su duba su dawo da wasu masu masauta da aka saukesu a gwamnatin ba.


To ka ga irin wadannan alkawuran da sauransu sun jawo masa farin jini kuma ya sanya mutanen jihar Bauchi duk da a lokacin tana da komai, ga gwamna, ga ‘yan majalisu ga komai amma al’ummar jihar Bauchi suka tunbuketa kamar yadda ake ciro rogo daga kasa. Sai kuma daga karshe kowa dai ya ga halin da ake ciki yanzu haka a jihar Bauchi idan ya cika alkawuran an sani idan bai cika ba ma mutanen Bauchi su ne masu hukunci.


Don haka al’ummar jihar Bauchi basu da wani dimuwa ko rashin fahimta na yadda za su yi zabe ko wanda za su zaba da yadda kuma za su kare abun da suka zaba har sai ka basu, wannan kuma tun 2015 ko 2019 ba, tun zamanin Isah Yuguda a 2007 jama’a suka tumbuke gwamnati wanda Malam Isah Yuguda yana zaune shi kadai ne jagora shi kadai ne fitacce ya kada gwamnatin Ahmadu Mu’azu ya tunbuketa daga kasa. Don haka jama’an jihar Bauchi wayayyo ne a fagen siyasa in ka musu daidai za ka ga daidai in ka musu rashin daidai ka jira lokaci za su maka rashin daidai.     


Bisa dogaro da irin wadannan muke da karfin guiwa a kan Ambasada Air Mashal Sadique Baba Abubakar don dan jihar Bauchi ne mai kishinta, kuma ya yi aiki a bangaren soja har ya kai kololuwa ya bauta wa kasa tsakani da Allah kuma ya samu yabo da jinjina daban-daban daga gwamnatin tarayya musamman daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zuwa yanzu suka kasance su ne hafsoshin Nijeriya da suka fi kowanne daxewa a kan karagar mulki kuma su na kammalawa bisa irin gudunmawar da suka bayar sai ya saka musu da kujeran Ambasada.


Duk mukamin da Saddique ya rike bai taba mancewa da jiha ba, yana can yana taimaka wa jiharsa ta Bauchi, ya taimaki ‘yan jihar, ya samar musu da ayyukan yi, ya kawo makarantar soja ya kawo asibiti an kawo filin jirgi na soja an kuma taimaki mutanen jihar Bauchi da yawa bisa doka.
Sannan kasancewarsa wanda ya karanci sashin mulki da kuma harkokin siyasa ya san yadda ya tafiyar da harkokin siyasarsa cikin mutunci da karamci. Wannan ya sanya jama’a suke masa kallon dattijo mai karamci, ko kalamansa na siyasa idan kana saurara za ka ji ya sha banban da na wasu, maganganu ne na hikima da ilimi da sanin ita kanta siyasar. Bisa cancantarsa da dacewarsa mu al’ummar jihar Bauchi muka kirashi da ya zo ya nemi gwamna kuma ya amince da yardar Allah kamar yadda Malam Isah Yuguda ya tumbuke gwamnati mai ci a 2007 da kuma yadda aka tumbuke gwamnati mai ci a 2019 muna da kyakkyawar zaton a demokradiyyance Air Mashal Sadik da goyon bayan al’ummar jihar Bauchi zai tumbuke wannan gwamnan bisa gazawar da ya yi wajen cika muhimman alkawuran da ya yi da kuma yadda ake tafiyar da gwamnatinsa a dukunkune ba a bayyane ba. 


Da yawan mutane ba su gane menene ya shiga ko menene ya fita ba, ni yanzu ko ya za ka yi da ni ba zan iya fada maka nawa ne yawan kudin albashin jihar Bauchi ba, saboda su da kansu suna canza alkalumomi daban-daban kan albashi, an kafa kwamitoci daban-daban kai har ta kai magaryar tikewa mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela ya jagoranci kwamiti a kan matsalar albashi da giratuti amma wai yanzu an dawo wai an yi wani kwamiti a karkashin sakataren gwamnatin jihar, kun ga irin wannan kwamacalar da ake yi, masu hankali a cikin jihar Bauchi suna kallonsu ne kawai.


Ya alakar Air Mashal da mambobin APC?


Sai sambarka. Shi kuma Air Masha Sadiq Baba tun da ya shigo jam’iyyar APC yake mutunta ‘yan jam’iyyar yake amsar shawarori yake jawo kowa a jika, kuma baida girman kai bai da tunkahon cewa shi ya fi kowa iyawa duk lokacin da ka zo masa da shawara zai saurareka, ga mutunta mutane ga alkairi da yake musu. Bisa matsalolin da suke jibge a jihar Bauchi muke ganin kamar shi gwamna mai ci ya zubar da damarmakin da ke da shi.


Bayan wannan ma kuma ya zo ya sake daukan wani tafiyar teku-da-yasa na neman shugaban kasa wanda aka masa mummunar kaye ya bata lokaci a maimakon ya yi amfani da wannan damar wajen daidaita lamura a jihar da nasa da jam’iyyarsa amma sai ya bari yanzu al’amura sun tabarbare a jam’iyyarsa, shi ma yana ta fama ne ta ina zai yi dumbuldunbul ya kai labara. Don haka muna tabbatar masa da illahirin al’ummar jihar Bauchi za mu yi amfani da tsarin doka da bin ka’idoji a demokradiyya wajen neman mutane a siyasance, ilmance, da hikimance za mu ayyana kura-kuran wannan gwamnatin da fito da alkairan Sadik Abubakar wanda muna da tabbacin jama’an jihar Bauchi za su yi na’am da Sadik.


Akwai kalubalen yadda wasu jiga-jigan APC irin su Sanata Halliru Jika, Sanata Lawan Gumau da wasu suka fice daga jam’iyyar ba ka gani hakan zai zama matsala ga Air Mashal Sadik?


Duk dan siyasa magana ta gaskiya ba zai so ya rasa koda mutum daya ba. Amma wani abun in ya faru sai ka ce tsautsayi ne ko kuma kaddara ya riga kata. Ni yadda nake gani musu, domin in sun fita ne bisa ra’ayin kashin kai to tsarin mulki ya basu damar hakan, amma dai ba za su fita da korafin danniya ko babakere ba. Domin zabe ne aka yi amfani da wakilai a idon duk duniya a gaban kowa, hatta su ‘yan takaran babu wani da zai ce maka an yi masa magudi sai dai mutum ya fadi son ransa. Don haka zaben fitar da gwani da aka gudanar na jam’iyyar APC an gudanar da shi bisa adalci da cancanta. Balle a ce jagoran jam’iyyar APC a jihar Bauchi Malam Adamu Adamu da shi da sauran jagorori irin su Yakubu Dogara ne suka zauna suka tilasta aka yi wani.
Zabe ne aka yi na mutum biyar-biyar a dukkanin gundumomi da muke da su sama da 323 suka yi wannan zaben a Zaranda a bayyanar jama’a suka zabi Air Mashal, to shi ya sa mutane masu kuri’a ba ‘yan siyasa ba, suke ganin zabinsa, zabi ne daga Allah domin an yi zabe sun gani ba wani korafi kafin da bayan zaben sai daga baya ne da wasu suka rasa kujerar suke fito da salo na daban, don haka ina bai wa wadanda suka fitan shawara su sake tunani su sake nazari domin duk abun da mutum zai fada ko ya ce.


Mu da mu aka kafa APC, na ajiye daraktan yada labarai na kasa don a yi a hadaka, amma yau sau uku ina shiga zabe a jere Allah (Madaukakin Sarki) bai bani nasara ba, kuma akwai dimbin mutane irina wadanda sun ma fi wadanda suka fitan nan wahala ga jam’iyya, sun fi cancanta na ilimi da wayewa, sun fi su mutane, amma su sun samu nasara sau da daman a zaben fitar da gwani kuma suka fito babban zabe suka tafi dukka a karkashin jam’iyyar nan ta APC yanzu bai kamata su gode wa Allah ba?, duk wanda bai gode wa ni’imar Allah ba, zai kuwa gode wa azabar Allah. Ba su da wani dalili na fita daga cikin jam’iyyar nan.


Kuma wani abun dadi, dukkanin wadanda suka fitan nan babu wanda Air Mashal bai ziyarta ya nemi mutane masu kima da suke tare da su duk don a rarrashesu a tafi tare ba, to muddin in su na yi don kishin jama’a da kishin jihar Bauchi don a ceto jihar daga halin da take ciki ne da basu fita ba kuwa. Ni a kashin kaina ina kallon fitarsu din nan akwai kuskure, musamman dan uwanmu, abokinmu, shugabanmu Sanata Halliru Dauda Jika da Sanata Lawan Yahaya Gumau wadannan mutune biyun mun kafa jam’iyya da su, don haka dole fitansu ya damemu don mun san dawainiyar da muka yi tare da su, mun kuma san irin alfarma da rufin asiri da wannan jam’iyyar ta musu wadanda da yawanmu ba mu samu ba kuma ba mu yi fushi ko jin kyashi ko daina binsu ba.


Don haka idan tura takai bango duk bibiyarsu da ake yi za a rabu da su. Abun da dai kowa ya kamata ya sani shine jam’iyya ba ta musu komai bai alkairi da karamci, don haka in sun fice ba zai shafi nasarar jam’iyyarmu ba.
Na san ‘yan jihar Bauchi da salon zabensu, tabbas ina tabbatar maka duk zamewar ‘yan siyasa muddin mulkin wani bai gamsar da su ba to sai sun cireshi, ‘yan siyasa dai za su cigaba da cece-kucensu, amma tabbas jama’an jihar Bauchi a shirye suke su cire gwamnati mai ci su kawo ta Air Mashal.


Ka yi maganar cewa gwamna Bala ya yi alkawura bai cika ba, wasu za su iya cewa ga ayyukan hanyoyi su na gani a zahirance me za ka ce a nan wannan?


Wadannan ayyukan ribar kafa ne kuma yanzu in ka dubesu kusan dukka sun tsaya ba wani wurin da ake cigaba da aiki, bilhasalima ni a unguwana ina son na fada maka titin da a kowani lokaci yana cikin farillan gwamnatin PDP shine wanda ya tashi daga shataletalen babban bankin kasa zuwa karshen Railway aikin ya tsaya ba a sanya wuta ba, ba a komai ba, ba a karasa aikin ba.
Kamar yadda ya zargi Muhammad Abdullahi Abubakar na kasa kara aikin a cikin shekara huxu, shi ma Bala Muhammad din ka ga ya ci shekara uku bai kammala wannan aikin ba. Aiki idan an kammala komai shine an gama, in ba a kammala ba sunansa ba a kammala ba sai dai a ce ya cimma wani mizani na aikin, wannan guda daya ma kenan fa nake fada maka wanda ya shafeni kai tsaye. Kuma a bisa bayanan da muke samu kusan dukkan fadin jihar abun da ke faruwa kenan, daman aikin nasa na titi ne to yanzu aikin ya tsaya. Kamfanoni da dama sun tsaya da aiki, ka ga mu yanzu wurinmu zan iya bugan kirji in ce ba a aikin tun da na gani kuma rahotonnin da suke fitowa duk labarin daya ne, wannan ma yana kara fusata mutane yana qara vata musu rai domin an riga an lasa wa mutane Zuma a baki kuma ba a qarasa ba ana son a basu madaci.


Meye harsashenka kan rikicin da ke faruwa a majalisar dokokin jihar Bauchi a halin yanzu?


Eh ba abun jin dadi ba ne. Daman tuntunin mun san tafiyar akwai munufurci a ciki, mun san tafiyar ana yi ne ba don Allah ba, yanzu ka ga kowa da aka yi wakiliya ka ga kowa abun da ya sa yake biyayya da abun da ya sa ya canza jam’iyya da yawansu sun ci amanar jam’iyyar da ta zabesu ta APC suka koma jam’iyyar APC wanda basu da wata dalili ta yin hakan. APC ta musu komai kuma tana zaman lafiya a Bauchi, suka zo suna bin gwamnan nan (na PDP) suka ce wai don kishin jihar Bauchi suke yi, to idan don gaskiya ne meye sa ba za su yi adalci su hakura ba don sun fadi a zabukan fitar da gwani ba? Mafiya yawansu sun fadi ne a zabukan fitar da gwani ba za su samu damar komawa majalisar ba shi ya sa suke ta fito da abubuwan nan haka, wannan shine gaskiyar magana. Idan biyayyar da suke yi da gaske ne meye sa ba za su karasa bin gwamnan ba don kishin jihar? Tun da jama’a sun saukaka musu sun je zaben fitar da gwani kuma sun fadi.


Magana ce kawai ta son kai, kuma jama’an jihar Bauchi ba ma damuwarsu ba kenan, abun da ke damun jama’an jihar Bauchi kawai shine suna jiran lokacin zabe ya zo su canza tun daga gwamna har wasu ‘yan majalisunsu. Mu abun da ke faruwa bai bamu mamaki ba illa dai suna kara tozartar da kansu a idon duniya su na fito da karanci da nuna kaskanci nasu wanda ba zai taimakesu ko ya taimaki jihar ba. 


A matsayin mafi yawa daga cikinsu mambobin jam’iyyarku ne wani shawara kake ba su?


Shawara ai nasu ne, sun tuntubi wadanda ya kamata su tuntuba ne suke yin abun da suke yi? Ka ga basu yi hakan ba ina tunani. Don haka ni a kashin kaina bana jin dadin abun da yake faruwa kuma ba zai taimaki demokradiyya ba, tun da tun a farko mun faxa musu cewa su tsaya a matsayin ‘yan adawansu, tun kuma lokacin da aka karya tsarin zabar shugaban majalisar muka ce musu in gwagwarmaya za ku yi ku doge ku dage har san an yi daidai to ka ga tun daga wajen aka fara samun matsala, don haka yanzu shawara ta rage musu. 

Leave a Reply