Uncategorized

Taya Murna Bisa Cika Shekara 6 A Karagar Mulki

A madadin ni kaina da iyalaina, ni Alhaji Abdul Ibrahim (Maitaman Misau/Jarman Akuyam) ina farin cikin taya mai martaba Sarkin Misau, Alhaji Alhaji Ahmed Suleiman, mni murnar cika shekara shida cif a bisa karagar mulkin masarautar Misau.

Ya mai martaba, ka maida mu abun alfahari bisa azamarka da himmarka gami da kwazonka, bisa na mijin kokarinka wajen ganin ka hidimta wa al’ummarka. A kowani lokaci muna alfahari da kai, tare da taya murna bisa wannan cika shekara shida bisa kwanciyar hankali da nasarorin da ka iya cimawa.

Muna farin ciki da lale da wadannan shekaru shidan, da fatan Allah zai kara maka lafiya da nisan kwana domin ka cigaba da faranta ran dubban daruruwan al’ummanka.

Rattaba hannu:

Alh. Abdul Ibrahim

(Maitaman Misau/Jarman Akuyam)

Leave a Reply