Uncategorized

Taya Murnar Cika Shekara 6 A Karagar Mulkin Masarautar Misau

A madadin ni kaina da iyalaina, ni Arch. Sadiq Ahmed Iliyasu (Walin Tunfure)Β nake shiga cikin ayarin dubban daruruwan al’umma wajen taya mai martaba Sarkin Misau, Alhaji Alhaji Ahmed Suleiman, mni murnar cika shekara shida cif a bisa karagar mulkin masarautar Misau.

Bisa himma da aikinka tukuru ne ya sanya aka samu dumbin nasarori, ina tayaka murna tare da maka fatan samun nasarori a nan gaba. Allah kara maka lafiya da nisan kwana.

Muna farin ciki da lale da wadannan shekaru shidan, da fatan Allah zai kara maka lafiya da nisan kwana domin ka cigaba da faranta ran dubban daruruwan al’ummanka.

Rattaba hannu:

Arch. Sadiq Ahmed Iliyasu

(Walin Tunfure)

Leave a Reply