‘Yan APC Dubu Bakwai Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Bauchi
Daga Khalid Idris Doya
Dan takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Adamu Dako tare da magoya bayansa sun ayyana ficewa daga jam’iyyar APC zuwa cikin jam’iyyar PDP.
Da ya ke jawabi a lokacin yankan katin shiga PDP a ofishin jam’iyyar PDP da ke karamar hukumar Bauchi jiya, Adamu Dako ya bayyana cewar abubuwa ba su tafiya daidai a cikin jam’iyyar APC don haka ne ya yanke shawarar ficewa, “Yau (Jiya) ni da magoya bayana sama da dubu bakwai (7,000) mun ayyana ficewa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
“Na kasance a da baya jagora a cikin jam’iyyar APC, amma cikin ikon Allah na fice daga jam’iyyar sakamakon matsaloli da suke jibge a cikinta. Na yi nadamar bata shekaru da shekaru a cikin jam’iyyar APC.”
Alhaji Dako ya ce, dukkanin alamun fadin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ya tabbata, yana mai cewa, hatta zabin da jam’iyyar ta yi wa dan takarar gwamnan Sadik Baba Abubakar alamu ne da ke nuna ba za ta iya samun nasara a zaben gwamnan jihar ba, “Wannan dan takara da jam’iyyar APC ta ayyana kalubale ne a gabanta a zaben 2023.”
“Duk wanda ya san yadda aka yi hadaka aka kafa APC, yanzu kowa ya san ba jam’iyya ake yi ba son zuciya kawai ake bi. APC ta mutu murus a jihar Bauchi. Na shigo jam’iyyar PDP da kyakkyawar manufa.”
Ya ce, sun shiga PDP ne lura da irin nasarorin da gwamnan jihar Bala Muhammad ya cimma na kyautata jihar, don haka ne ya nuna kwarin guiwarsa na cewa Gwamna Bala zai sake samun nasara a karo na biyu tare da kiran al’umma da su mara wa gwamnan ba.
Da yake amsar wadanda suka sauya shekar, Shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Bauchi, Alhaji Abdulkadir Alin Bababa, ya sanar da cewa, jam’iyyar ta karbi sabbin mambobin jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP su dubu bakwai.
Shugaban wanda ya samu wakilcin, mataimakinshi Sani Ahmad, tare da sauran shugabanin jam’iyyar a karamar hukumar Bauchi, ya bai wa wanda suka dawo jam’iyyar tabbacin samun adalci daga wajensu tare da share musu hawayen matsalolin da suka zo da su, ya rokesu da su taimaka domin samun nasarar PDP a 2023.
Shi ma a jawabinsa na lale ga sabbin mambobin, babban mai bai wa gwamnan jihar Bauchi shawarori kan harkokin siyasa, Hon. Abubakar Faggo, ya bayyana cewar yadda ake shigowa cikin jam’iyyar PDP alumu ne dake nuna irin gamsuwa da salon mulkin gwamna Bala.
Ya ce, tabbas gwamna Bala Muhammad na gudanar da kyawawan ayyukan bunkasa jihar Bauchi, don haka ne ya nemi jama’an jihar da su kara bashi dama domin kyautata jihar, ya kuma nuna cewa tabbas wadanda suka dawo jam’iyyar za su samu goyon baya daga PDP.
Faggo ya nuna cewa jam’iyyar APC bata kyauta wa mambobinta, don haka ne ma suke ta komawa cikin PDP, “Mu a PDP akwai adalci, don haka kun zo lallai kuma za a muku adalci.”
Da ya ke maida martani kan wannan matakin, jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC a jihar Bauchi, Alhaji Adamu Aliyu Jalla, ya ce suna da ja man cewa mutum 7,000 sun fice daga jam’iyyarsu.
Ya ce, kowa na da ‘yancin sauya sheka, amma ya ce da dandazon mutum kaza fita wannan kuma akwai bukatar tabbatarwar kafin aminciwa, “farfagansar siyasa ce kawai. Mutum dubu bakwai wasa ne. Mu ba mu da bayanin cewa wannan adadin sun fita a jam’iyyunmu. Don haka muna kalubakantarsa da ya bayyana sunayen mutum dubu bakwai din.”
Ya ce babu gaskiya na cewa ana gudanar da mulki cikin jam’iyyar APC bisa rashin adalci, ya nuna cewa suna da karfin da za su iya cin zaben 2023 tare da goyon bayan al’ummar jihar.