Uncategorized

YANZU-YANZU. Tsohon Dan Takara Shugaban Kasa, Bashir Tofa Ya Kwanta Dama

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi.
Allah ya yi rasuwa wa tsohon dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar National Republican Convention (NRC) a 1993 Alhaji Bashir Othman Tofa.

Tofa ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.

Wata majiya ta tabbatar wa BAUSHE Times labarin rasuwar a safiyar yau Litinin a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AATH).

An haifi marigayi Malam Bashir Othman Tofa ne a ranar 20 ga watan June na shekarar 1947.

Marigayi ya yi karatun Firamare dinsa ne a Shahuci Junior Primary Kano kuma ya yi makarantar gaba da Primary a Kano.

Leave a Reply