Uncategorized

Za’a fara gasar musabaqar Al’qur’ani a garin Misau.

Daga: Mohammed Kaka Misau


A wata sanarwa ta musamman da kwamitin shirya musabaqa na musamman karkashin jagorancin Mal. A. B Yarima Bawu ya fitar a yau Juma’a 20/01/2023 ya bayyana cewa za’a fara gasar Musabaqar Al’qur’anin ne daga ranar Asabar 28/01/2023 da misalin karfe Tara na safe.

Kwamitin ya Kara da cewa za’a rufe Musabaqar a ranar Lahadi 29/01/2023 da misalin karfe hudu na yamma a dakin taro na gidauniyar Cigari dake cikin garin Misau.

Mal. Bawu shine ya dauki nauyin shirya gasar Musabaqar da zummar zaburar da Matasa wajen ganin sun Kara azama da riko da Al’qur’ani Mai girma.

Ana sa ran za’a samu halar ta mutane da dama wajen budewa da rufe wannan gasa.

Leave a Reply