Uncategorized

Zaben Gwamnan Bauchi: Bala Na Gaba-gaba

  • Saura Kananan Hukumomi 2 Kowa Ya San Inda Ya Dosa

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Bauchi da ke ci a halin yanzu kuma dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin lemar PDP, Bala Abdulkadir Mohammed na kan gaba da a kan manyan abokan karawarsa biyu a yayin zaben gwamna da ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a ranar Asabar.

Zuwa lokacin aiko da wannan rahoton da karfe 10pm na ranar Lahadi sakamakon zaben da aka tattara daga kananan hukumomi 18 cikin 20 na jihar Bauchi na nuni da cewa Bala Muhammad ya samu nasara a cikin kananan hukumomi 12 zuwa yanzu.

Sakamakon da aka gabatar a gaban babban malamin tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Bauchi, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, mukaddashin shugaban jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutse ta jihar Jigawa, ya nuni da cewa sauran kananan hukumomi biyu a kammala tattara sakamakon.

Kazalika, dan takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya samu nasara ne a kananan hukumomi 6 kacal zuwa yanzu.

Sai dai wakilinmu ya nakalto cewa sauran kananan hukumomi biyun da suka rage na Bauchi da Toro manyan kananan hukumomi ne da suka fi kowace karamar hukuma tulin kuri’u.

Wakilinmu ya labarto cewa Bala ya samu nasara ne a kananan hukumomi Jama’are; Kirfi; Bogoro; Warji; Itas Gadau; Shira; Zaki; Ganjuwa; Dass; Alkaleri; Ningi; da kuma karamar hukumar Tafawa Balewa.

Yayin da shi kuma Air Marshal na APC ya samu nasara a cikin kananan hukumomin Giade (karamar hukumarsa); Gamawa; Darazo; Misau; Katagum da kuma karamar hukumar Dambam.

Kawo yanzu dai ana zaman jiran sauran kananan hukumomin Bauchi da Toro yayin da aka tafi hutu.