Uncategorized

Gwamna Bala Ya Samu Gagarumar Nasara A Karamar Hukumarsa

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Bauchi kuma dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad ya samu gagarumar nasara a karamar hukumarsa a zaben gwamna da ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar ranar Asabar.

Mohammed ya lashe zaben ne karamar hukumarsa ne da kuri’u dubu 34,387 yayin da dan takarar APC Air Marshal Sadique Baba Abubakar ya samu kuri’u 15,798 a Alkaleri.

Sakamakon zaben da aka gabatar ranar Lahadi wa babban baturen tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya nuna cewa Halliru Dauda Jika na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 2,069 ne kacal a karamar hukumar Alkaleri.

Kawo yanzu dai gwamna Bala ne ke kan gaba da rinjaye masu tulin yawa.

Leave a Reply