Uncategorized

Ambaliyar Ruwa Ya Tursasa Wa Magidanta 200 Kauran Dole A Kirfi

Daga Idris Shehu Zarge

Rahotonni sun tabbatar da cewa sama da magidanta dari biyu ne da suke mazauna karamar hukumar Kirfi da ke jihar Bauchi suka yi kaura na dole daga gidajensu sakamakon wani ambaliyar ruwa mai tsanani da ya riskesu a ‘yan kwanakin baya da suka wuce.

A yayin mamakon ruwa kamar da bakin kwaryan, al’umman yankin sun rasa dukiyoyinsu, gonakai da kuma dabbobinsu wanda aka kiyasce ya zarce na miliyoyin naira.

A yayin ziyarar jajantawa a yau din nan, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar da hadin guiwar ‘yan majalisun dokokin jihar za su duba hanyoyin da suka dace domin kawo tallafi ga wadanda lamarin ya shafa, yana mai cewa wannan babban abin jajantawa ne ga jama’an.

“Za mu gidaya asarar da aka yi na gidaje da gonakai domin ganin mun kawo muku tallafi. Ina tabbatar muku za a kawo muku tallafi.”

Daga nan, gwamnan ya jajanta wa al’ummar da suka yi kauran dole bisa wannan matsalar da ya samesu, yana mai nemansu da su sauwala komai ga Allah domin ganin ababen da suka rasa ya dawo musu cikin amincewar Allah.

Ya ce, za su yi kokarin ganin sun bi hanyoyin da suka dace wajen ganin gwamnatin tarayya ta kawo dauki ga al’ummar da ambaliya ya yi wa barna a jihar Bauchi.