Dan Majalisar Wakilai na Shira/Giade Ya Taya Gwamna Bala Mohammed Murnar Cika Shekaru 67

Daga Mohammed Kaka
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Shira/Giade a Majalisar Tarayya, Hon. Sani Ibrahim Tanko, ya shiga sahun ‘yan Najeriya da ke taya Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir (Kauran Daular Usmaniyya), murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara ta 67.
A wata hira ta musamman da aka yi ta wayar tarho, Hon. Sani Ibrahim Tanko ya mika sakon taya murna ga Gwamna Bala Mohammed tare da yabawa da irin salon shugabanci da gwamnan ke gudanarwa a matsayinsa na jagora na gaskiya.
“Muna matukar godiya a mazabar Shira/Giade bisa irin gudummawar da kuka bayar a bangaren ilimi, jin dadin al’umma, lafiya, da kuma tallafawa matasa da marasa galihu a fannoni daban-daban,” in ji shi.
“Kun taimaka wa talakawa ba kawai a cikin birane ba, har ma da kauyuka. A ko’ina akwai ayyukanku da kowa ke gani da idonsa. Muna kara godiya gare ku, Mai Girma Gwamna,” Hon. Tanko ya kara da haka.
Ya kuma yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da kare Gwamnan tare da ba shi nasara wajen cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.