Uncategorized

2023 Bauchi: Yayyaga Allunan Tallar Nura Soro Abun Kunya Ne, Inji Rahama

Shugaban kungiyar matasan APC ta APC Youth Progressives Forum, Honorable Ukkasha Hamza Rahama, ya ce yayyaga allunan tallar dan takarar gwamnan Bauchi a jam’iyyar APC, Alhaji Nura Manu Soro abun tir da kunya ne, yana mai cewa kowa na da ‘yancin fitowa a dama da shi na neman kujerar siyasa.

“Mun wayi gari da ganin an yayyage hotunan allon ‘yan takara musamman na Nura Manu Soro wanda wasu mutane suka dauki nauyin yi. Wannan abun tir da Allah wadai ne. Wannan kuma ya faru ne a daidai lokacin da Nura Manu Soro yake da cikakken ikon fitowa takara bisa damar da dokar kasa ta ba shi.”

Rahama wanda ke bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a ofishin Correspondents’ Chapel da ke Bauchi a ranar Laraba, ya bayyana cewar wasu da suke zargin magoya bayan gwamnati mai ci ne a jihar sun bi hotuna da allunan tallar ‘yan takara inda suka yayyaga na jam’iyyun adawa musamman na APC, ya misalta hakan a matsayin abun kaico.

Rahama ya bukaci Gwamnan Jihar Bala Bala Muhammad da ya gaggauta dakatar da wasu matasan da suka kama yayyaga hotunan allunan ‘yan takara na jam’iyyun adawa a fadin jihar, yana mai cewa barin hakan ba zai haifar da sakamakon mai kyau ga shirin zaben 2023 ba.

Rahama yana mai cewa bai dace a samu irin wannan ta’adin a jihar Bauchi ba, lura da yadda jihar ta kware a siyasance da kuma wayewa a fagen siyasa, don haka ne ya nemi hukumomin da abun ya shafa da su tashi tsaye domin yi wa tufkanci warwara.

“Muna kira ga gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad a matsayinsa na shugaba da ya tsawatar tare da tashi tsaye domin magance wannan matsalar na rusa allunan tallar ‘yan takara na jam’iyyar adawa (APC), hakan ne zai nuna wa al’umma cewa zaben 2023 zai gudana ba tare da kokarin tauye hakkin wasu ba.”

Rahama ya bukaci hukumomin tsaro da su kama masu irin wannan aikin domin tsarkake jihar daga yunkurin take hakkin wasu ko Neman kawo baraka a zaben 2023 da ke tafe, “Kuma tabbas gwamna ya dace ya sanya baki don a bar yin irin wannan ta’asar.”

“Sanann muna kira ga kwamishinan ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su tabbatar da an cafko wadanda suka aiwatar da hakan domin kiyaye faruwar wannan lamarin a nan gaba. Hakan ne zai sanya kowa ya ji ba a kokarin tauye masa hakki ko musguna wa jam’iyyun adawa ko ‘yan takararsu,” inji Honorable Ukkasha Hamza.

Leave a Reply