Uncategorized

2023: Gwamnatina Za Ta Tabbatar An Ci Moriyar Man Fetur Na Bauchi Da Gombe – Tinubu

  • Zan Yaki Matsalar Rashin Aikin Yi A Nijeriya, Ya Shaida

Daga Khalid Idris Doya

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, a karkashin gwamnatinsa ne al’ummar jihohin Gombe da Bauchi za su shaidi yadda za a fara cin gajiyar albarkatun Mai da Allah ya azurta jihohin da su domin cigaban kasar nan da farfado da tattalin arziki.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 yana mai yin wannan alkawarin ne a lokacin da ke kaddamar da yakin zabensa a jihar Gombe ranar Litinin, ya ce muddin jama’a suka zabe shi, tabbas za a fara morar albarkatun Mai din da aka samu a Arewa Maso Gabas wanda ya tabbatar da cewa kasar nan za ta amfana da hakan matuka lura da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu.

Ya ce bayan aikin Mai da zai maida hankali a Arewa Maso Gabas, zai tabbatar da samar da ayyukan yi wadanda za su fitar da miliyoyin matasa daga cikin talauci da fatara. Ya kuma ce, a ba su dama domin su baje fasaharsu wajen saita kasar nan.

Tinubu yana mai cewa ta hanyar inganta lamuran tattalin arziki ne za a samu mafita kan matsalolin da suke addabar kasar nan. Don haka ya nemi alfarmar al’ummar jihar Gombe da su fito kansu da kwarkwararsu su zabeshi a matsayin shugaban kasa, kana su zabi Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnansu a karo na biyu tare da sauran ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a jihar.

Ya kuma yaba da irin kokarin da ya ga Inuwa ya yi a jihar a zamanin mulkinsa na farko.

Leave a Reply