Uncategorized

Ban Bai Wa Gombawa Kunya Ba – Inuwa Yahaya

Daga Khalid Idris Doya

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kuma dan takarar Gwamnan Jihar Gombe, ya ayyana cewar, shi kam yana alfahari da cewa bai baiwa al’ummar jiharsa kunya ba domin ya zage damtse ya gudanar da ayyukan raya jihar da har ake alfahari da shi.

Ya ce, ayyukan da ya shimfida su ne za su zama masa asasi wajen sake zama gwamna a zaben 2023 da ke tafe.

Inuwa ya shaida hakan ne a lokacin da ke jawabi yayin kaddamar da yakin zaben Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Litinin a Jihar, ya kara da cewa al’ummar Gombe sun Yi alkawarin za su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa, da shi a matsayin gwamna hadi da sauran ‘yan takara.

Muhammadu ya ce ko yanzu aka ja layin zaben a jihar ya tabbatar zai ci zabensa babu hamayya domin Gwambawa su na tare da shi.

A kan hakan ya shelanta wa al’ummar jihar cewa Idan suka zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa zai daura daga inda Buhari ya tsaya domin kara nausa kasar nan zuwa mataki na gaba.

Ya yi amfani da wannan damar wajen gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa muhimman ayyukan da ya aiwatar a jihar da ma Arewa Maso Gabas baki daya.

Daga nan sai ya roki al’ummar jihar da su zabi APC a dukkanin matakai.

A nasa jawabin, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Alhaji Kasim Shettima, ya tabbatar wa al’ummar Gombe cewa APC za ta rike amana kuma za ta yi kokarinta wajen shawo kan matsalolin da suke akwai muddin aka sake ba ta dama.

Ya yi shelanta wa al’ummar arewa Maso Gabas cewa muddin suna son aikin halo Mai da aka samu a Gombe da Bauchi ya tabbatar, to su amince su sake zabin APC domin su ne suka san yadda za su yi a fara lasar albarkatun Mai din.

Leave a Reply