Uncategorized

2023: Zan Shayar Da Al’ummar Mazabar Misau/Dambam Romon Demokrudiyya Muddin Aka Zabeni, Inji Aliko


Daga: Mohammed kaka Misau

Dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Misau/Dambam da ke jihar Bauchi Mohammed Aliko Mohammed, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takara a majalisar wakilai ta tarayya a zaben shekara ta 2023, tare da shan alwashin samar da ribar demokradiyya ga al’ummar mazabarsa da zarar ya dale karaga.

BAUSHETIMES ta nakalto cewa, Aliko, wanda sanannen dan siyasa ne a fadin jihar Bauchi zai tsaya takarar ne karkashin jam’iyyar APC kuma tuni ya sayi fom na nuna sha’awar sa ta tsayawa takara.

Aliko ya ce ya yanke shawarar tsayawa takarar ne lura da cewa yana da dukkan kwarewar da zai gudanar da kyakkyawar jagoranci wa al’ummarsa muddin ya zama zababbe.

Mohammed ya ce zai yi amfani da kwarewar da ya samu na zamowar sa ma’aikacin Gwamnati kuma cikakken dan siyasa domin tabbatar da cewa ya bautawa al’ummarsa.

Kazalika, ya yi alkawarin samar da romon dimokuradiyya wa al’ummar tasa ta fuskar samar da ayyukan yi wa matasa da mata na yankin nasa.

“Lura da irin kwarewar da nake da ita na aiki da fannoni daban-daban zan yi amfani da ita wajen tabbatar da cewa mazabata ta Misau/Damban ta yi fice wajen ababen cigaba a fadin jihar Bauchi har ma da kasa baki daya.

“A yau na dauki wata turba mai girma wacce nake da yakinin cewa za mu yi amfani da ita wajen samar da ingantacciyar madora ga al’ummar yankinmu.”

Idan za a iya tunawa dai mahaifin sa Alhaji Aliko Mohammed Dan’iyan Misau sanannan jagora ne kuma masanin harkar kudi a fadin kasa baki daya, wanda ya tallafawa mutane da dama ta fuskar kasuwanci da sana’o’i sun tsaya da kafafun su.

Leave a Reply