Uncategorized

A SHIRYE NAKE DOMIN CIGABADA TAIMAKAWA KUNGIYOYI : HON BAKOJI BOBBO

Mohammed Kaka misau.

A yunkurinshi na cigabada bada tallafi wa kungiyoyi masu zaman kansu a karamar hukumar Misau, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Bauchi Hon Bakoji Aliyu Bobbo ya kaddamar da rabon hotunanshi da Mai girma Gwamnan jihar Bauchi Sen. Bala Muhammad Abdulkadir tare da Shugaban jami’iyyar PDP na jihar Bauchi, Alh. Hamza Koshe Akuyam wa masu KEKE- NAPEP 32 a wannan Juma’a, awani mataki don kara tallata jami’iyyar shi ta PDP a karamar hukumar Misau.

Shugaban masu rinjayen ya kaddamarda rabon fastocinne alokacinda ya karbi bakwancin ‘Yayan kungiyar “Keke Napep Riders Association” inda kuma ‘yayan kungiyar suka manna wa kekunan su wadannan hotuna don nuna goyon baya da kara tallata hajar sa da na dukkan wadanda ke tare dashi saboda taimako da kuma tallafi da yake bawa wannan kungiya a dukkanin abubuwan da suka taso.

Hon Bakoji Aliyu ya kuma bayyana Jin dadin sa tare da kara bada tabbacin cigaba da tallafi wa wannan kungiya don ganin ta samu cigaba, inda ya kara tabbatar wa shuwagabannin kungiyar aniyarsa na cigaba da basu tallafi da Kuma yi musu kokari gurin cin gajiyar duk wani tsari na gwamnati da zata yi wanda ya shafi sana’ar su.

Shugaban masu rinjayen yace ya kuma ware wani kaso na musamman wa dukkanin wadannan mutane bisa karamci da suka nuna masa wanda zai ringa basu aduk wata saboda suma su samu hanyar cigaba da yin sana’ar su cikin walwala. Ya kara bayyana cewar a Koda yaushe kofa a bude take idan akwai wani tallafi da kungiyar ke nema zaiyi iya bakin kokarin sa gurin ganin ya taimaka

Daga karshe ya kuma bada umarnin kara buga wadannan hotunan don kara wa wannan kungiya kamar yadda suka bukata, kana yayi godiya tare da bada kudade wa wannan kungiya don raba wa wadannan mutane bisa karamci.

Anashi jawabin, Shugaban kungiyar “Keke Napep Riders Association” na karamar hukumar Misau Malam Kawu Anana ya bayyana wannan kudiri a matsayin gudumawa da zasu bawa Hon Bakoji Aliyu Bobbo ta hanyar sana’ar su gurin tallata siyasar sa kamar yadda Shima yake musu abubuwan alkhairi Yau da kullum.

“A Koda yaushe muna shirye gurin shiga cikin hidimar sa a dukkan abunda ya taso. Zamu shiga lungu – lungu, sako – sako da wadannan hotuna don ganin mun isar da Sakon dake dauke a jiki.”

Kungiyar ta kuma nemi Minority Leader ya kara buga Mata wadannan hotuna don wasu da suke bukata da basu samu ba suma a Saka musu.

Shima anashi tsokacin, Shugaban jami’iyyar PDP na karamar hukumar Misau, Abdu Haruna Sirko ya bayyana Bakoji Aliyu Bobbo a matsayin jajircecce dake kare mutuncin jami’iyyar PDP a Koda yaushe wanda shine daya tilo dake zaune a cikin Al’ummah Yau da kullum a cikin Wakilai da aka zaba a karamar hukumar Misau.

Ya kara da cewa abubuwan da yake yi wasu kananan hukumomi ma suna fada idan sun hadu da mutanen su a gurin harkar jami’iyya , inda suke cewa “Hon. Bobbo wakili ne mai kwazo da son cigaba wanda kullum muna ganin sa a cikin mazabar sa yana zaune cikin mutanen sa, baya gudun Al’ummah…”

Leave a Reply