Hausa

Matawalle Ya Umarci Hafsoshin Tsaro Su Dira Sokoto Don Murkushe ‘Yan Fashin Daji Arewa Maso Yamma

Ƙaramin ministan tsaron ƙasar nan, Bello Muhammed Matawalle ya nuna damuwarsa kan ƙaruwar aikace-aikacen ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji a Jihar Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi.

Kan hakan ministan ya umarci shugabannin hafsoshin tsaro da su dira jihar Sotoko da nufin kawo karshen ‘yan ta’adda a Sokoto, Katsina, Zamfara da jihar Kebbi. 

A wata sanarwar da daraktan ya labarai na ma’aikatar Henshaw Ogubike, ya ce wannan yunkurin an ɗauka ne domin kawo karshen ‘yan ta’adda da suka adabi yankunan musamman Bello Turji da ‘yan tawagarsa.

Matawalle dai ya asha alwashin murkushe ‘yan fashin daji da kokarin farfaɗo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso yammacin kasar nan.

Leave a Reply