SABUWAR JIHAR BAUCHI: GWAMNA BALA YA KADDAMAR DA SABBIN AYYUKA.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar da sabbin ayyukan fadada manyan hanyoyi a fadar jiha.

Da yake jawabi yayin taron, Gwamna Bala Muhammad yace gwamnatinsa zata cigaba da samar da ayyukan inganta jiha don ganin ta tafi daidai da zamani tare da shiga sahun tsarorinta.

Hanyoyin da za’a fadada sun hada da;

  • Hanyar da ta tashi daga shatale-talen Dogon Yaro zuwa Otel din Zaranda
  • Awala zuwa Yuli
  • Awala zuwa filin tashi da saukar jirage na Sir Abubakar Tafawa Balewa

Dukkanin hanyoyin za’a rubanya su tare da sanya musu fitullu na zamani.

Taron kaddamarwan ya samu halartar Shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da kuma shugaban jam’iyyar PDP ta Kasa Yarima Uche Secundus da mataimakin sa na shiyyar Arewa Sanata Nazif Suleiman Ibrahim da sauran manyan baki.

A jawabansu daban Uche Secondus da Aminu Tambuwal yabawa gwamna Bala Muhammad suka yi kan jajircewa wajen samar da ayyukan inganta jihar Bauchi duk da halin kuncin karancin kudin shiga da ake fama da shi.

Har wa yau sun yabawa gwamnan kan inganta dimokradiyya ta hanyar aiki kafada da kafada da jam’iyun adawa musamman Yan majalisar dokoki ta jiha da na tarayya ba tare da la’akari da bambance bambance ba.

Shima a nasa tsokacin, kakakin majalisar dokoki ta jiha Hon Abubakar Suleiman cewa yayi majalisar za ta cigaba da marawa gwamnatin baya wajen aiwatar da ayyukan ciyar da jihar Bauchi gaba.

Taron ya samu halartar jami’an gwamnati da kuma sarakuna da shugabannin addinai.

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani
Laraba, 16, Disamba, 2020.

%d bloggers like this: