Hausa

Kuri’ar Amincewa: Masarautar Kaltungo Ta Yaba Wa Gwamna Inuwa Yahaya Bisa Kyakkyawan Shugabancinsa

Masarautuar Kaltungo ta bayyana cewa tana goyon bayan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya kuma za ta ci gaba da baiwa gwamnatin sa cikakken hadin kai da goyon baya.

Mai Martaba Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Mohammed ne ya bada wannan tabbacin yayin taron majalisar masarautar da sauran masu ruwa da tsaki a fadarsa.

Mai Kaltungo yace ya gayyaci masu rike da sarautun a fadarsa ne don gode wa Allah bisa damina mai albarka, da kwanciyar hankali da ci gaba a masarautar Kaltungo.

Masarautar ta ce taron ya zama wata manuniya na gamsuwar shugabannin al’umma daban-daban, bisa ayyukan ci gaba a yankin a cikin shekaru 2 na gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a Jihar Gombe.

“Kamar yadda kowa ya sani, bikin mrnar amfanin gonakin namu ya samo asali ne tun tale-tale don cin abinci da sayarwa a cikin al’ummomin mu kamar yadda al’adar mu ta bukaci mu hadu mu ci tare, tare da talakawan mu a fada kafin kowa ya fara cin amfanin gonar sa tare da ‘yan uwa; wannan shi ne dalilin da yasa muka bukaci yin amfani da babban taron bikin don yin bitar halin da alummar mu ke ciki a Kaltungo dangane da yadda ake gudanar da mulki a Jihar Gombe.

Yayin da yake yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Kaltungo, ya ce babban abin alfahari na ayyukan raya kasa da ake gani a masarautar Kaltungo da Jihar Gombe baki daya ba abin mamaki bane, saboda ya samo asali ne daga siyasa da shugabanci na gari.

Ya kara da cewa albarkar amfanin gona da aka samu a Masarautar Kaltungo yana da alaka da ingantaccen yanayin tsaro wanda ya bawa manoma damar zuwa noma ba tare da taraddadi ba.

“Duk mun san halin da tsaro ke ciki a kasar nan a yanzu, amma muna godiya ga Allah cewa gwamna Inuwa Yahaya ya samu damar wanzar da zaman lafiya a cikin jihar mu baki daya don bada damar wanzwar ci gaba. Muna farin cikin hakan kuma muna yaba masa saboda kokarin da yake yi.

Basaraken gargajiyan ya shaidawa manema labarai cewa aikin titi kamar wanda ya ratsa Billiri zuwa Kamo zuwa Awak da Dogon ruwa da gyara babban asibitin Kaltungo da sauran kananan asibitoci na gundumomi dake Kaltungo ayyuka ne da suka cancanci yabo.

“Ra’ayoyin da shugabannin al’ummomin mu suka bayar a yau sun nuna gamsuwa da mutanen mu sukayi kan yadda wannan gwamnati ke aiki, kuma alkiblar al’umma ta ita ce tawa, don haka ina son in tabbatar muk cewa masarautar Kaltungo tana goyon bayan wannar gwamnati”.

Wasu hakimai da sauran masu rike da sarautu wadanda suka gabatar da jawabai a yayin taron na masu ruwa da tsaki suka ce, bangaren ilimi yana samun sauyi cikin hamzari ta hanyar gine-gine da fadada makarantu, musamman daga darajar makarantar sakandaren gwamnati ta Bangunji ya zuwa babbar makarantar gwamnatin Jihar Gombe.

Suka ce gina gadar Lalaipido a cikin garin Shongom wanda ta kashe rayuka tsawon shekaru wadda gwamnatin Inuwa Yahaya ta yi abun a yaba ne.

“Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya dawo da martabar ƙananan hukumomin mu tare da dora su akan kyakkyawar turba, sabanin a baya lokacin da wasu daga cikinsu ba sa iya ko biyan albashi daga baitulmalin su”.

Leave a Reply