Hausa

Matsalar tsaro za ku tunkara ba ‘Black Friday’ ba —Shehu Sani ga Hisbah

Tsohon Sanatan Jahar Kaduna Sen. Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci hukumar Hisbah ta jihar Kano game da ‘Black Friday’.

A ranar Juma’a hukumar ta gargadi dukkan ’yan kasuwa da su gujewa amfani da kalmar ‘Black Friday’ wajen tallar kayayyakinsu.

Shehu Sani ya ce hakan da hukumar ta yi shirme ne, inda ya ja hankalin ta da ta mai da hankali wajen kashe-kashe da garkuwa da ake yi a yankin Arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa, ranar Juma’a babbar rana ce ga musulmai, amma yana ganin cewa babu komai dan an kira ta da wani suna.

Shehu Sani ya kara da cewa an fi bukatar Jami’an Hisbah a filin daga, inda ya kamata a ce sun magance matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa.

Leave a Reply