Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Biyar: Sharudan Abubuwan da suke karya Azumi

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Abubuwa masu karya Azumi da suka gabata, idan ka cire Jinin Haila da na Biki, – wato su ne saduwa da mace (Jima’i), fitar da maniyyi, ci da sha, abin da yake da ma’anarsu, kaho, janyo amai – ba sa karya Azumi sai da sharuda guda uku:

Na farko: Mutum ya zama yana sane da cewa suna karya Azumi. Amma idan ya zama ya jahilci cewa; suna karya Azumi to Azuminsa bai karye ba. Saboda hukuncin yana faduwa bisa jahilci. Allah ya ce: {Ya Ubangijinmu kar ka kama mu da abin da muka manta ko muka yi kuskure} [al-Baqarah: 286]. Ya tabbata a Hadisi Allah ya ce: ((Na yi)). Muslim (126).
Haka kuma Allah ya ce: {Babu laifi a kanku a abin da kuka yi kuskure, sai dai kuna da laifi ne a abin da zuciyarku ta yi gangancinsa} [al-Ahzab: 5].

Don haka duk wanda ya kasance jahili ya aikata wani abu mai karya Azumi cikin rashin sani da kuskure to Azuminsa bai karye ba, sawa’un ya jahilci hukuncin ne, kamar ya yi zaton wannan abu ba ya karya Azumi, sai ya aikata shi, ko kuma lokacin ya jahilta bai san lokacin ya yi ba, kamar ya yi zaton al-fijr bai fito ba, sai ya ci abinci, alhali ya keto, ko ya yi zaton rana ta fadi, sai ya aikata daya daga cikin wadancan abubuwa, alhali rana ba ta fadi ba, to wannan Azuminsa bai karye ba, saboda ya tabbata Sahabi Adiyyi bn Hatim (ra) a lokacin da Ayar: {Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183] ta sauka, kawai sai ya dauki zare guda biyu, daya baki daya fari, sai ya ajiye a kasan filonsa, jim kadan sai ya duba su, yana ta cin abincinsa, har sai da ya iya banbance tsakaninsu, bayan gari ya yi haske, a lokacin tukun ya dena cin abinci. Sai da safe ya tafi wajen Manzon Allah (saw) ya ba shi labarin abin da ya yi, sai Annabi (saw) ya ce: ((Lallai filonka yana da fadi in dai har farin zare da bakin za su kasance a karkashinsa. Ai abin da ake nufi kawai shi ne, hasken yini da duhun dare)). Bukhari (4509, 4510), Muslim (1090).
To ka ga a nan Adiyyi ya ci abinci bayan fitowan alfijir, amma Annabi (saw) bai umurce shi da ramuko ba, saboda bai san hukuncin yadda ya kamata ba.
Ya tabbata daga Asma’u bnt Abbubakar (ra) ta ce: ((Mun yi buda baki a zamanin Annabi (saw) a ranar da aka yi gajimare, sai daga baya rana ta fito)). Bukhari (1959).
Asma’u ba ta fadi cewa; Annabi (saw) ya umurce su da rama Azumin ranar ba, ba su san lokaci bai yi ba suka yi buda baki. Da a ce ya umurce su da ramuko da an ruwaito.
Sai dai da zaran an fahimci rana ba ta fadi ba, to sai a kame baki, har sai ranar ta fadi.
Haka wanda ya ci abinci bayan fitowan al-fijr, yana zaton bai fito ba, sai daga baya ya bayyana masa cewa; al-fijr ya fito to Azuminsa ya inganta, kuma babu ramuko a kansa, saboda bai san lokaci ya yi ba.

Kuma Allah ya halasta wa mutum ya yi ta ci da sha, da Jima’i, har sai al-fijr ya keto, ba a ramuko ga abin da aka ba da izni a kansa. Amma da zaran mutum ya san cewa; lokacin ya yi to sai ya kame daga cin ko shan.

Sharadi na biyu: Ya kasance mutum yana tune ba mai mantuwa ba. Idan ya aikata daya daga cikin abubuwan da suka gabata cikin mantuwa, to shi ma Azuminsa bai baci ba. Saboda Ayar Suratu al-Baqarah da ta gabata.
Kuma ya tabbata daga Abu Huraira (ra), daga Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya manta ya ci ko ya sha alhali yana Azumi to ya cika Azuminsa, kawai Allah ne ya ciyar da shi ya shayar da shi)). Bukhari (1933), Muslim (1155).
Sai Annabi (saw) ya yi umurni da cika Azumin, wannan kuwa dalili ne a kan Azumin bai baci ba. Jingina ciyar da shi da shayar da shi ga Allah shi yake nuna Allah ba zai kama shi a kan haka ba. Amma duk lokacin da mutum ya tuna sai ya kame ya dena ci, ya tofar da na bakinsa, saboda uzurin nasa ya kauce.

Sharadi na Uku: Ya kasance bisa zabinsa da nufinsa ya aikata dayan wadancan abubuwa ba tilasta shi aka yi ba. Idan tilasta shi aka yi to Azuminsa bai baci ba, don haka babu ramuko a kansa, saboda Allah ya dauke hukunci a kan wanda ya kafirta bisa tilastawa, alhali zuciyarsa tana nitse da imani, inda Allah ya ce: {Duk wanda ya kafirce da Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta, alhali zuciyarsa tana nitse da imani, amma wanda ya sake zuciyarsa ga kafirci to akwai fushin daga Allah a kansu, kuma suna da azaba mai girma} [al-Nahl: 106].
Idan Allah ya dauke hukuncin kafirci daga wanda aka tilasta to wanda aka tilasta a kan abin da bai kai kafirci ba shi ya fi cancanta a dauke masa hukuncin.
Idan miji ya tilasta wa matarsa ya sadu da ita alhali tana Azumi, to Azuminta bai baci ba, kuma babu ramuko a kanta. Shi kuma bai halasta ya tilasta mata saduwa da ita ba, alhali tana Azumi, sai dai idan Azumin nafila ne ba tare da izninsa ba, alhali yana gari, to a wannan shi ba abin zargi ba ne, yana da uzuri.

Idan kura ko garin mai nika ko wani abu ya shiga cikin mai Azumi ba tare da nufinsa ba, ko ya yi kurkuran baki ko shaqa ruwa a hanci, amma sai ya wuce ya shiga cikinsa, ba da nufi ba, Azuminsa bai baci ba, kuma babu ramuko a kansa.

Saka kwalli, ko saka magani a ido ba ya karya Azumi, ko da mutum ya ji dandanonsa a makokwaronsa, saboda wannan ba abinci ko abin sha ba ne, ba kuma abin da yake ma’anarsu ba ne. Haka Azumi ba ya baci don an diga magani a kunne, ko saka magani a rauni, ko da an ji dandanonsa a makokwaro.

Haka Azumi ba ya baci idan mai girki ya dandana a harshensa don jin gishiri, matukar bai hadiye ba. Haka Azumi ba ya baci idan an shanshana turare, kuma ba ya baci idan an kurkure baki, ko shaqa ruwa a hanci, sai dai kar mutum ya shaqa ruwan sosai, don kar ya wuce ya shiga cikinsa. Annabi (saw) ya ce: ((Ka shaqa ruwa a hanci sosai, sai dai idan ka kasance mai Azumi)). Abu Dawud (2366), Tirmiziy (788), Nasa’iy (87), Ibnu Majah (407).

Haka yin aswaki ba ya karya Azumi, kai, Sunna ne ma yin aswaki da rana. Amir bn Rabee’a (ra) ya ce: ((Na ga Annabi (saw) sau ba iyaka, yana yin aswaki alhali yana Azumi)) Abu Dawud (2364), Tirmiziy (725).
Don haka amfani da aswaki shi ya fi a kan yin amfani da makilin da brush.

Babu laifi ga mai Azumi ya yi abin da zai saukaka masa tsananin zafi da kishirwa, kamar jika jiki da ruwa da makamancin haka, kamar yadda aka ruwaito hakan daga wasu Sahabbai.

Saboda haka wajibi ne bawa ya san hukunce-hukuncen Ibada da yake yi ma Allah, don ya yi ibada kamar yadda Allah yake so, kuma ya yarda da ita.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita aiyukan da’a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al’umma da tausayin talakawa.

Leave a Reply