Uncategorized

Zaben 2023: Ni da Jama’a ta Munyi Mubaya’a wa Abdul Ningi- Alh. Dandija misau

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi

Wani jigo a siyasar Jihar Bauchi Alh Ibrahim Dan Dija Misau ya bayyana mubaya’ar sa wa me neman takarar kujerar sanata a Yankin Bauchi ta tsakiya, Sanata Abdul Ahmed Ningi.

Dan Dija ya bayyana mubaya’ar tasa ce a sa’ilin da tawaga Mai karfi ta sanata Abdul Ahmed Ningi suka kai masa ziyara da rokon iri a gidan sa dake garin Misau a ranar lahadi.

Dan Dija yace shi da tasa tawagar zasu mara baya domin ganin sanata Abdul Ahmed Ningi ya kaiga nasara a zabe me zuwa na 2023.

Ya kara da cewa Sanata Abdul Ahmed Ningi yayi rawar gani a baya domin Al’umma da dama sun sheda irin ababe na romon dimokuradiyya da ya Samar, a saboda haka ya bukaci nasa magoya bayan da suzo a tafi tare a tsira tare

Kwamitin wadanda suka hada da Hon. Baidu Misau , Babangida Ahmed (Katukan Misau) Alh Ladan Darazo, Alhaji Magaji Nasaru, Hon. Wakili Abdu Misau, ADC da Magayakin Miya sun kai ziyara ta musamman ce domin neman goyon bayan sa a tafiyar Abdul Ahmed Ningi.

Leave a Reply