Da Dumi-Dumi: Zabbaben Mambar Majalisar Dokokin Kaduna Ya Rasu
Daga Khalid Idris Doya
Zababben mamba mai wakiltar mazabar Chikun a Majalisar Dokokin jihar Kaduna, Hon. Madami Garba Madami, ya rasu.
Ya rasu ne da safiya ranar Asabar sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana ba a wani asibiti a Kaduna.
Kodayake zabbaben dan Majalisar ya amshi shaidar lashe zabe daga wajen hukumar zabe ta kasa (INEC) biyo bayan samun nasarar da ya yi a babban zabe 2023, amma bai samu zarafin halartar bikin kaddamar da majalisar Dokokin jihar da ya gudana a ranar 13 ga watan Yunin 2023 ba sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita wacce a karshe ma ta yi ajalinsa.
Masu jaje da ta’aziyya wadanda suka ziyarci gidansa da ke Barnawa, sun misalta rasuwar tasa a matsayin wacce ta jijjiga su matuka. Su na addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Marigayi Madami ya taba zama Shugaban karamar hukumar Chikun kuma tsohon Kwamishina ne a jihar kafin ya fito takarar kujerar Majalisar wanda ya kayar da dan Majalisar da ke kan kujerar a mazabar ta Chikun a zaben da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris a karkashin jam’iyyar PDP.
Babban dan siyasa a karamar hukumar wanda ke wakiltar mazabar Chikun/Kajuru a Majalisar wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Umar Yakubu Barde, da kuma tsohon mambar Majalisar Dokokin jihar da ya wakilci mazabar Chikun, Hon. Ishaku Chawaza, dukkaninsu sun yi alhini da jajen rasuwar zababben dan Majalisar, su na masu misalta rasuwar tasa a matsayin rashi mai zafi.
A cewarsu, “Rasuwar Madami babban rashi ne, shi din mutum ne mai nagarta kuma mai biyayya wa jam’iyya, muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kurakuransa.