Uncategorized

Kotu Ta Umarci A Bar Lauyoyi Da Iyalan Emefiele Suke Ganawa Da Shi

Daga Khalid Idris Doya

Wata babban Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya (FCT) ta umarci daraktan hukumar tsaron farin kaya ta (DSS), Yusuf Bichi, da ya sanar da dama yadda Lauyoyi da iyalan dakataccen gwamnan babban Bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele za su ke samun zarafin ganawa da ziyartar shi ba tare da wani tangarda ba.

Kotun da ke zamanta a gundumar Maitama karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu, a ranar Juma’a, ta ce, Emefiele na da ‘yanci kamar yadda dokar kasa ta tanadar masa na samun zarafin ganawa da shi.

Umarnin na zuwa ne bayan bukatar da Lauyan Emefiele, J.B. Daudu, SAN, ya shigar da ke nuna cewa, DSS ta kasa basu amsa kan wasikun bukatar ganawa da ziyartar wanda yake karewa mai kwanan wata 14 watan Yunin 2023.

Lauyan wanda ake kara na biyu da na uku, I. Awo, Esq, ya ce ba su da wata masaniyar cewa DSS ta hana ko yin watsi da bukatun ganinsa, kuma ma hana ganawa da shi din ai bai dace ba.

Daga bisani, Awo ya nuna kwarin guiwarsa na cewa hukumar tsaron za ta mutunta umarnin kotu ta kyale lauyoyinsa da iyalansa ziyartarsa.

Kazalika, ofishin Antoni-janar na tarayya ba su yi suka kan bukatar ba.

Kodayake, dukkanin lauyoyin DSS da na ofishin Antoni-janar na tarayya sun bukaci a basu wadataccen lokaci kan bada martaninsu kan asalin bukatar.

Kotun ta amince da bukatar, inda ta dage zaman zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2023 da za a saurari hakikanin karar.

Leave a Reply